Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, a wani zaman taro da ya hada bangarorin musulmi an tattauna batun hadarin da ke tatatre da yaduwar akidar wahabiyanci da kuma yadda yake illa wajen ruguza akidar muslunci da kum akoyarwasa da bata sunan muslunci a idon duniya baki daya.
Kungiyar gwagwarmayar kasar Lebanon ta hzib ullah ta yi kakakusar suka da yin Allawadai da kai harin da jami’an tsaro gami da ‘yan bangar masarautar Baharain suka yi kan gidan sakataren jamiyar wifaq ta kasar Bahrain, a yankurin mahukuntar tare da taimakon AMURKA DA Saudiyya suke yi na ganin sun murkushe masu neman sauyi.
B bayan watsa wani labari da ke cewa masarautar kasar Bahrain na shirin kama shugaban majalisar malaman addinin muslunci ta kasar Ayatollah Sheikh Isa Kasim majalisar ta ja kunnen masarautar da ta shiga taitayinta dangane da duk wani mataki da za ta dauka kan wannan bakar aniya.
Wanann mataki da masarautar kasar Bahrain ke neman dauka kan shehin malami baya rasa nasaba da irin kiran da yake yi ne ga mahukuntan da su saurari bukatun mutane domin warware takaddamar da ake fama da ita, maimakon yin amfani da karfin tuwo wajen murkushe fararen hula masu neman hakkokinsu da aka haramta musu. 1105045