Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo, cewa kafofin yada labarai na kasashen musulmi za su iya taka gagarumar rawa wajen wayar da kan musulmi kan muhimamna bubuwa da suke faruwa a duniyar musulmi musamman ma kan batun p[alastinu da kuma halin da al’ummar wannan yanki suke ciki na zalunci da mamayar yahudawan sahyuniya.
Wasu daga cikin masana sun yi imanin cewa farkawar da al’umma ta yi a wannan zamani hakan jefa gwamnatin kasar Amurka cikin wani yanayi na rudu da rashin sanin makomar lamurra domin kuqwa ka iya Amurka da tsarinta na jari hujja rushewa, musamman ma ganin cewa hatta mutanen kaasar Amurka ba a bar su baya wajen nuna rashin amincewa da wannan tsari na zalunci da ke tafiyar da kasarsu.
Tun bayan da mutanen kasashen larabawa suka fara bore a arewacin Afirka al’ummar Amurka ta mike tsaye wajen ganin ita ma ta kwato hakkokinta, yayin da kuma ita gwamnatinsu ta ke ganin ta yi babbar asara ta wasu daga cikin shugabannin larabawa masu kare manufofinta musamman a Masar da Tunisia, lamarin da har yanzu ba ta san inda ya dosa ba.
Farkawar da al’umma ta yi a wannan zamani hakan jefa gwamnatin kasar Amurka cikin wani yanayi na rudu da rashin sanin makomar lamurra domin kuqwa ka iya Amurka da tsarinta na jari hujja rushewa a lokuta masu zuwa a nan gaba, domin kuwa duniya ta gaji da zaluncin Amurka.
1105797