IQNA

An Gudanar Da Wani Taro Na Nuna Goyon Baya Ga Manzon Allah A Gabacin Saudiyya

23:44 - September 28, 2012
Lambar Labari: 2421511
Bangaren kasa da kasa, an gudanar da wani taro mai taken goyon baya ga manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalan gidansa tsarkaka a yankin katif da ke gabacin kasar Saudiyya wanda mabiya tafarkin mazhabatr iyalan gidan manzon Allah da ke yankin suka dauki nauyin shiryawa da gudanarwa.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanr gizo cewa, an gudanar da wani taro mai taken goyon baya ga manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalan gidansa tsarkaka a yankin katif da ke gabacin kasar Saudiyya wanda mabiya tafarkin mazhabatr iyalan gidan manzon Allah da ke yankin suka dauki nauyin shiryawa da gudanarwa.

Daruruwan mutanen a birnin Riyad na kasar Saudia ne suka gudanar da zanga zanga a kusa da wani kurkuku a bayan garin inda suke neman a saki yan’uwansu fursinonin siyasa wadanda hukumomimin kasar suke tsare da su shekaru aro aro.

A zanga zanga na jiya Alhamis dai yansanda sun fasa taron masu zanga zangar kuma sun kama da dama daga cikinsu. A ranar litinin da ta gabata ma, jami’an tsaro a kasar ta Saudia sun kama masu zanga zanga da dama a kusa da kurkukun na Tafiya kusa da Lardin Qassim a cikin birnin. Tun cikin watan Febrerun shekarar bara ne dai gwamnatin kasar ta saudiyya take fama da borin mutanen kasar musamman a yankin Qadif da Awamiyya inda suke bukatar ta saki fursinonin siyasan da take tsare da sub a tare da gabatar da su a gaban kotu ba na tsawon shekaru masu yawa.
Kungiyoyin kare hakkin bil’adam ada dama a duniya sun tabbatar da cewa hukumomin kasar ta Saudia suna tsare mutanen na lokuta masu tsawo kan ra’ayinsu na siyasa.

1107640









captcha