Kmafanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar talabijin din Al-alam cewa, yan ta’addan kasar Syria da suke dauke da makamai kuma suke samun goyon bayan kasashen yammacin turai sun kashe dan rahoton gidan talabijin press TV daga birnin Damascus fadar mulkin kasar a lokacin da yake cikin bayar da rahoto kai tsaye ga tsashe.
AS bangre guda kuma daya daga cikin kwamandojin 'yan tawayen Siriya da tawagarsa da suke yaki domin kifar da gwamnatin kasar sakamakon tallafin makamai da kudade da suke samu daga kasashen waje ya sanar da cewa shi da tawagarsa sun dawo cikin sahun rundunar sojin gwamnatin kasar.
A taron manema labarai da ya gudanar a birnin Damaskas a jiya laraba tare da tawagarsa Captain Khalid Abdur-Rahman Azzamil ya bayyana cewar shi da tawagarsa sun yanke shawarar dawowa cikin sahun rundunar sojin gwamnatin Siriya, tare da gudanar da aiki da ma'aikatar gudanar da sulhu tsakanin 'yan kasa, bayan sun balle daga rundunar sojin kasar tun bayan fara zanga zangar neman aiwatar da gyare-gyare a harkar siyasar Siriya watanni 18 da suka gabata.
Captain Khalid Abdur-Rahman ya jaddada cewar amfani da makamai, ayyukan ta'addanci ta hanyar kai hare- hare kan gine- ginen gwamnati da aiwatar da kisan gilla kan fararen hula da sojojin gwamnati, ba zasu taba warware matsalar kasar Siriya ba, don haka sun yi nadama kan kura-kuren da suka aikata, tare da dawowa karkashin rundunar sojin gwamnati domin yin hidima wa kasa.
Bayan ballewar Captain Khalid Abdur-Rahman da tawagarsa daga rundunar sojin gwamnatin Siriya, shi ne ya rike matsayin mataimakin shugaban Majalisar Soji a yankin kudancin kasar Siriya karkashin kungiyar 'yan tawayen kasar da suke kiran kansu da Jaishul-Hur.
1108036