IQNA

Mahukunta Birnin Paris Sun Hana Musulmi Gudanar Da Zanga-Zanga

17:02 - October 01, 2012
Lambar Labari: 2423854
Bangaren kasa da kasa, mahukuntan birnin paris fadar mulkin kasar Faransa sun hana musulmi gudanar da jerin gwano domin nuna rashin amincewarsu da cin zarafin da ake yi wa addinin muslunci a cikin kasashen turai da hakan ya hada da ita kanta kasar ta Faransa.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na saphirnews, cewa mahukuntan birnin paris fadar mulkin kasar Faransa sun hana musulmi gudanar da jerin gwano domin nuna rashin amincewarsu da cin zarafin da ake yi wa addinin muslunci a cikin kasashen turai da hakan ya hada da ita kanta kasar ta Faransa da kuma wasu kasashen na daban.
A wani labarin kuma an ware wasu makudan kudade da suka kai dalar Amurka miliyan saba’in domin gudanar da ayyuak na musamman da suka shafi muslunci a kasar Malzia a cikin kasafin kudi na wannan shekara da nufin bunkasa harkokin addinin muslunci a fadin kasar, wadda take daya daga cikin kasashen musulmi.
A wani baynin kuma an gudanar da taron baje klin kur’ani a India, a wajen taron na bajen kolin an nuna kwafi-kwafi na kur’ani mai tsarki wadanda aka rubuta da hannu a kasashen musulmi daban-daban, haka nan kuma wadanda aka buga su a kasashen musulmi, da nufin kara fito da matsayin wannan littafi mai tsarki, tare da bayyanawa duniya cewa matsayinsa yana damfare ne da rayuwar mabiya addinin muslunci, domin ya zama hannunka mai sanda ga masu keta alfarmarsa.
Gudanar da taron baje koli na kasa da ake yi a kasar Pakistan inda ake nuna wasu daga cikin manyan kwafin kur’ani mai tsarki a ginin babbar cibiyar yada al’adun muslunci da ke birnin Lahor na kasar, na dag acikin muhimamn ayyuka da gwamnatin kasar pakistan ke aiwatarwa akowace shekara. Amma a wannan shekara lamarin ya dauki sabon salo na kara kawata taron, da kuma yawan kur’anan da ake nunawa.
1109439

















captcha