IQNA

Palastinu Ta Halarci Taron Kungiyar UNESCO A matsayin Mai Cin Gishin Kai

16:56 - October 03, 2012
Lambar Labari: 2425466
Bangaren kasa da kasa, kungiyar bunkasa harkokin ilimi da al'adu ta kasa da kasa ta gayyaci bangaren palastinawa domin halartar taronta wanda kuma suka halarta kamar kowace kasa mai cin gishin kanta bayan da kungiyar ta amince da palastinu a matsayin kasa mai yanci tun shekarar da ta gabata.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na UNESCO, cewa kungiyar bunkasa harkokin ilimi da al'adu ta kasa da kasa ta gayyaci bangaren palastinawa domin halartar taronta wanda kuma suka halarta kamar kowace kasa mai cin gishin kanta bayan da kungiyar ta amince da palastinu a matsayin kasa mai yanci tun shekarar da ta gabata lamarin day a bakantawa Amurka matuka.

Wani rahoton kuma ya tabbatar da cewa kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya zai fara aiwatar da shirinsa na gudanar da bincike kan rikicin kasar Mali a cikin wannan wata na Oktoba. Wakilin kasar Guatamala a Majalisar Dinkin Duniya da a halin yanzu kasar ce ke jagorantar shugabancin kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya na karba karba ya bayyana cewar a cikin wannan wata na Oktoba da muke ciki ne kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya zai fara aiwatar da shirinsa na gudanar da bincike kan rikicin kasar Mali, kuma muhimman batutuwan da kwamitin tsaron zai gudanar da bincike kansu sun hada da batun take hakkin bil-Adama, fataucin mutane da na makamai zuwa cikin kasar ta Mali da kuma matsalar tsananin talauci da ke addabar al'ummar kasar. A gobe alhamis 4 ga watan Oktoba ne ake sa ran za a fara gudanar da zaman sharen fage kan matsalolin da suke addabar kasar Mali, kuma tuni gwamnatin Mali ta gabatar da bukatar neman tura dakarun kasa da kasa zuwa cikin kasarta ga kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya domin taimaka mata a kokarin da take yi na ganin ta kwato yankunan arewacin Mali daga hannun masu tsaurin kishin Islama.


1112178
captcha