Bangaren kasa da kasa, shugaban kungiyar jihadulIslami ya jadda cewa babu gudu babu ja da baya a matsayin da suka dauka na gwagwarmaya da yahudawan sahyuniya har sai sun kwato am al’ummar palastinu dukaknin hakkokinsu da yahudawan sahyuniya suka hana su kuma suke ci gaba da murkushe su.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar talabiji din Al-alam, cewa shugaban kungiyar jihadulIslami ya jadda cewa babu gudu babu ja da baya a matsayin da suka dauka na gwagwarmaya da yahudawan sahyuniya har sai sun kwato am al’ummar palastinu dukaknin hakkokinsu da yahudawan sahyuniya suka hana su kuma suke ci gaba da murkushe su da karfin tuwo tare da taimakon kasashen turai.
A wani labarin kuma tsagerun yahudawan sahayoniya 'yan kaka gida suna ci gaba da kai hare hare kan Palasdinawa tare da musguna musu a yankunan da suke gabar yammacin kogin Jordan. Kafar watsa labaran Palasdinawa ta Wafa ta bayyana cewar a yau asabar tsagerun yahudawan sahayoniyya 'yan kaka gida sun kai farmaki kan Palasdinawa tare da lalata musu gonaki ta hanyar sare bishiyoyin 'ya'yan marmari da yawansu ya kai a yankin Alkhadar da ke kudancin garin Baitu- Laham a gabar yammacin kogin Jordan.
Har ila yau tsagerun yahudawan sahayoniyyan 'yan kaka gida sun kai farmaki kan kauyen Kufru-Kadoum da ke gabar yammacin kogin na Jordan da nufin barnata gonakin Palasdinawa, amma al'ummar kauyen sun kalubalance su lamarin da ya janyo dauki ba dadi a tsakanin bangarorin biyu. A mafi yawan lokuta sojojin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila suna yin rakiya ga tsagerun yahudawan tare da katangen Palasdinawa da suke kokarin hana yahudawan barnata musu gonaki.
1113611