IQNA

Yahudawan Sahyuniya Sun Canja Sunayen Wasu Tituna A Birnin Qods

17:00 - October 06, 2012
Lambar Labari: 2426771
Bnagaren kasa da kasa, yahudawan sahyuniya sun canja sunayen wasu daga cikin tituna na birnin Qods wanda hakan yake a matsayin wani mataki na tsokana da mayar da palastinawa saniyar warea acikin dukkanin lamarin yankin tare da tabbatar wa duniya cewa yankin na yahudawa ne.
Kmafanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo, cewa yahudawan sahyuniya sun canja sunayen wasu daga cikin tituna na birnin Qods wanda hakan yake a matsayin wani mataki na tsokana da mayar da palastinawa saniyar warea acikin dukkanin lamarin yankin tare da tabbatar wa duniya cewa yankin na yahudawa ne ban a palastinawa ba.
Tsagerun yahudawan sahayoniya 'yan kaka gida suna ci gaba da kai hare hare kan Palasdinawa tare da musguna musu a yankunan da suke gabar yammacin kogin Jordan. Kafar watsa labaran Palasdinawa ta Wafa ta bayyana cewar a yau asabar tsagerun yahudawan sahayoniyya 'yan kaka gida sun kai farmaki kan Palasdinawa tare da lalata musu gonaki ta hanyar sare bishiyoyin 'ya'yan marmari da yawansu ya kai 120 a yankin Alkhadar da ke kudancin garin Baitu- Laham a gabar yammacin kogin Jordan. Har ila yau tsagerun yahudawan sahayoniyyan 'yan kaka gida sun kai farmaki kan kauyen Kufru-Kadoum da ke gabar yammacin kogin na Jordan da nufin barnata gonakin Palasdinawa.
Amma al'ummar kauyen sun kalubalance su lamarin da ya janyo dauki ba dadi a tsakanin bangarorin biyu. A mafi yawan lokuta sojojin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila suna yin rakiya ga tsagerun yahudawan tare da katangen Palasdinawa da suke kokarin hana yahudawan barnata musu gonaki domin zalunci.
1113564


captcha