Bnagaren kasa da kasa, jagoran juyin juya halin muslunci na kasar Ayatollah Sayyid Ali Khamenei yana gudanar da wata ziyarar rangadia wasu yankunan kasar domin ganawa da al’umma da jin matsalolinsu da kuma ganawa da jami’ai na wadannan yankunan.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwana yanar gizo na tashar Ala’alam, cewa jagoran juyin juya halin muslunci na kasar Ayatollah Sayyid Ali Khamenei yana gudanar da wata ziyarar rangadia wasu yankunan kasar domin ganawa da al’umma da jin matsalolinsu da kuma ganawa da jami’ai na wadannan yankunan kamar dai yadda rahoton ya yi nuni.
Jagoran juyin juya halin Musulunci a nan Iran Aya. Sayyeed Aliyul Khaminaee ya kai ziyara zuwa lardin Khorasan ta arewa a safiyar yau laraba. A cikin jawabin da ya gabatar a garin Bojnod cibiyar lardin Khurasan ta arewa, jagoran ya tabo batutuwa da daman a ciki da da kuma wajen kasar. Da yake magan a kan takunkumin tattalin arzikin da kasashen turai suka kara tsanantawa kan kasar Iran a cikin watannin na, jagoran ya bayyana cewa wannan ba sabon abu bane, don Jamhuriyar Musulunci ta Iran tana cikin takunkumi fiye da shekaru 30 da suka gabata. Don haka kasar Iran zata tsallaka wannan takunkumin kamar yadda ta tsallaka na baya.
Jagoran ya yi kira ga jami'an gwamnatin kasar Iran da su kara himma wajen kawo karshen tsada da kuma wasu wahalhalun da mutanen kasar suke fuskanta a cikin kwanakin nan. Jagoran a wani bangare na jawabinsa ya bayyana cewa kasashen Amurka da Turai wadanda su ma suke fama da matsalolin tattalin arziki mai tsanani a cikin kasashen su basu dorawa kasar Iran takunkumi don shirinta na makamacin Nuclear kamar yadda suke fada ba. Manufar wadannan kasashe shi ne ganin bayan tsarin Musulunci wanda yake jagorantar kasar tun fiye da shekaru 30 da suka gabata.
1117345