IQNA

Ci Gaba Da Kisan Gilla Kan Fararen Hula A kasashe Daban Daban

15:46 - October 29, 2012
Lambar Labari: 2439944
Yawan mutanen da suka rasa rayukansu sakamakon hare haren ta'addanci da aka kai sassa daban daban na kasar Iraki a cikin kwananki biyu kacal sun haura 65 tare da jikkatan wasu da dama.
A bayanin da majiyar tsaron kasar Iraki ta fitar ta fayyace cewar hare haren ta'addanci ta hanyar tada motoci da aka makare da bama bamai da kuma harba makamai masu linzami a garuruwan Mada'in, Ba'akuba da yankin Kazimiyya da ke arewacin birnin Bagadaza a jiya lahadi sun lashe rayukan mutane akalla 67 ciki har da 'yan sanda tare da raunata wasu 37 na daban.
Wadannan hare haren ta'addanci sun zo ne kwana daya bayan da hare haren wuce gina da iri da aka kai sassa daban daban na kasar Iraki musamman garin Sadar da ke arewa maso gabashin birnin Bagazada, inda hare haren suka lashe rayukan Irakawa 49 tare da jikkatan wasu 63 na daban.
A gefe guda kuma jami'an tsaron kasar Iraki sun yi nasarar kame wasu gungun 'yan ta'adda su 20 da ake nema ruwa a jallo kan zargin hannu a kai hare haren ta'addanci a yankunan garin Mosel da ke lardin Nainawa da ke arewacin kasar Iraki a jiya Lahadi.


1127340
captcha