IQNA

A Yau Dole A Yi Da Iran A Harkokkin Da suka Shafi Kasashen Duniya

9:25 - November 11, 2012
Lambar Labari: 2445936
Bangaren siyasa :Limamin juma'ar birnin Tehran ya bayyana cewa: Amerika da yan amshin shatanta dole su sani cewa; a yau yanayi ya canja kuma iran ta yi karfin da dole a yi da ita a harkokin da suka shafi kasashen duniya kuma matukar aka yi watsi da Iran to dole a samu tangarda da kuma samin cikas a harkokin da ake son cimmawa.



Kamfadin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin da suka shafi kur'ani mai girma a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa:Limamin da ya jagoranci sallar juma'a a birnin Tehran ya jaddada yin kira ga jami'an gwamnatin Iran da al'ummar kasar wajen kara kaimi domin rusa makircin makiya na kakaba takunkumi da barazana kan kasar Iran. A hudubar sallar juma'arsa a yau a babban Masallacin birnin Tehran Ayatullahi Ahmad Jannati ya yi nuni kan irin barazana da kakaba takunkumin da kasashen yammacin Turai ke yi kan kasar Iran, inda ya bayyana cewar tun tsawon shekaru 33 da suka gabata makiya da kasashen yammacin Turai suka taso al'ummar Iran gaba ta hanyar kakaba takunkumi kan kasarsu don haka takunkumin baya bayan nan da suka kakaba kan kasar ta Iran ba wani sabon abu ba ne. Ayatullahi Jannati ya kara da cewar kakaba takunkumi da gudanar da barazana da makiya ke yi, ba zasu taba yin tasiri a kan al'ummar Iran ba da suka lashi takwabin kare tsarin Jamhuriyar Musulunci, kuma al'ummar Iran zasu ci gaba da tafiya a kan kyakkayawar tafarkinsu, sannan kara samun wayewa da fadaka a tsakanin jami'an gwamnati da al'ummar kasa zai sanya kakaba takunkumi da barazanar da ake yi su kara zama wata babbar dama ta ci gaba da kara habakar Jamhuriyar Musulunci ta Iran.

1134696
captcha