Bangaren siyasa:kakakin ma'aikatar harkokin wajen jamhuriyar musulunci na Iran dangane da rashin tsantsantar Amerika na zama mamba a komitin kare hakkokin dan adam na majalisar dinkin duniya ya bayyana cewa; gwamnatin amerika ta aikata wasu mnya manyan laifuka masu munin gaske na take hakkin dan adam da kuma suka sabawa duk wani ma'auni na hankali da na kare hakki da mutunta dan adam da kuma dokokin da majalisar dinkin duniya da suka shafi dan adam.
Kamfadin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin da suka shafi kur'ani mai girma a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: kakakin ma'aikatar harkokin wajen jamhuriyar musulunci na Iran dangane da rashin tsantsantar Amerika na zama mamba a komitin kare hakkokin dan adam na majalisar dinkin duniya ya bayyana cewa; gwamnatin amerika ta aikata wasu mnya manyan laifuka masu munin gaske na take hakkin dan adam da kuma suka sabawa duk wani ma'auni na hankali da na kare hakki da mutunta dan adam da kuma dokokin da majalisar dinkin duniya da suka shafi dan adam.Kakakin ma'aikatar harkokin wajen ta Iran Mehman Paraest ya kara da cewa a yau idan aka yi la'akari za a ga cewa duk wani rikici da take hakkin dan adam gwamnatin Amerika nada hannu a cikinsa yawanci kuma it ace ke ruwa da tsaki wajan hanna kawo karshen duk wani take hakkin dan adam a duniya da kuma hana dokokin kare hakkokin bil adama yin aiki a mataki na kasashe da na yanki da na kasa da kasa da hukumomi da kungiyoyi don haka Amerika bai dace ba Amerika ta zama mamba a komitin kare hakkin dan adam na majalisar dinkin duniya.
1134688