Mataimakin shugaban kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon, Sheik Na’im Qasim ya yi kakkausar suka ga rahoton baya-bayan nan da babban sakataren MDD Ban Ki Moon ya fitar dangane da kudurin kwamitin tsaron majalisar mai lamba 1559 kan kasar Labanon.
Sheikh Na’im Qasim wanda ya ke magana a wajen wani biki da kungiyar ta shirya ya bayyana cewar Ban Ki Moon din cikin wannan rahoto nasa yana magana ne da yawun HKI don cimma manufofinta. Sheik Qasim ya ce Ban ki Moon din ya bayyana tura jirgi mara matuki da kungiyar Hizbullah ta yi cikin HKI a matsayin neman fada da kuma keta hurumi alhali kuwa ya yi shiru dangane da keta hurumin kasar Labanon da HKI take ci gaba da yi a kusan kullum.
Na’ibin shugaban Hizbullah din ya kara da cewa har ila yau Ban ki Moon ya rufe ido dangane da ci gaba da mamaye yankunan kasar Labanon da HKI take yi da kuma ci gaba da wuce gona da iri a kan yankuna daban-daban na kasar inda ya ce idan da a ce sun dogara ne da MDD wajen ‘yanto yankunan kasar Labanon da yahudawan sahyoniyan suka mamaye da kuwa ba su ‘yanto ko da wani bangare na wadannan yankunan ba.
1135670