IQNA

Ta'addanci Da Wuce Gona Da Irin HKI Kan Palasdinawa

12:49 - November 18, 2012
Lambar Labari: 2450328
Akalla bapalasdine guda ne ya rasa ransa a ci gaba da kai hare hare a yankin Gaza wanda jiragen yakin HKI suke kaiwa kimani kwanaki 5 da suka gabata.
Ya zuwa yanzu dai kimanin Palasdinawa 48 aka tabbatar da shahadarsu a yankin na Gaza a yayinda wasu 500 kuma suka ji rauni.
Tun ranar laraba da ta gabace sojojin HKI suka tsokano yaki da Palasdinawa a lokacinda suka kai hari kan motar Ahmad Al-Jabiri komandan dakarun Izzuddeen qassam na kungiyar Hamas suka kashe shi.
A wannan sabon yankin da HKI take kaiwa kan Palasdinawa a yankin Gaza dai, a karon farko Palasdinawa sun sami nasara cilla makaman linzami kan birnin Telavib babban birnin HKI, kuma makaman linzami sun daki majalisar dokokin HKI sun kuma kai yankunan da yahudawa suke zaune a birnin Qudus.
Har'ila yau a karon farko dakarun Palasdinawa sun sami nasara kakkabo jirgen yakin HKI samfurin F-16 guda daya da kuma na wanda bai da matuki shima guda daya .
Wadannan hare haren dai sun rikita al-amura da dama a cikin haramtacciyar kasar a karon farko a tarihin kasar.

1138751
captcha