Wani sabon harin wuce gona da iri da jirgin saman yakin sojin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila ya kai kan yankin Zirin Gaza ya yi sanadiyyar shahadar Palasdinawa 5 tare da jikkatan wasu fiye da 35 na daban a safiyar yau Litinin. Majiyar asibitin Palasdinawa ya bayyana cewa: A safiyar yau Litinin jirgin saman yakin sojin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila ya kai harin ta'addanci kan yankin Hayyuz-Zaitun da ke Zirin Gaza, inda ya yi sanadiyyar shahadar Palasdinawa 5 biyu daga cikinsu kananan yara, tare da jikkata wasu fiye da 35 na daban da suka hada da mata da kananan yara. Har ila yau majiyar ta Palasdinawa a yankin Zirin Gaza ta fitar da sanarwar cewa; A hare haren zaluncin da sojojin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila suka kai kan yankin na Gaza a jiya Lahadi sun yi sanadiyyar shahadar Palasdinawa 31 kuma 9 daga cikinsu iyalan gida daya ne, tare da raunata wasu da dama. Tun daga ranar Laraba da ta gabata 14 ga wannan wata na Nuwamba da sojojin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila suka fara kai hare haren wuce gona da iri kan yankin Zirin Gaza zuwa safiyar yau Litinin, Palasdinawa fiye da 80 ne suka yi shahada da suka hada da kananan yara da mata, yayin da wasu fiye da 700 na daban suka samu raunuka, baya ga rusa gine-gine da suka hada da gidaje da ma'aikatu gami da cibiyoyi.
1139824