Taron tattaunawar sulhu kan kasar Siriya da aka gudanar a birnin Tehran na kasar Iran ya cimma matsayar kafa kwamitin tuntuba da zai dauki alhakin shawo kan dukkanin bangarorin al'ummar Siriya. A taron manema labarai da ya gudanar a karshen zaman taron tattaunar sulhu kan kasar Siriya da aka gudanar a birnin Tehran na kasar Iran a jiya Lahadi; Ministan harkokin wajen kasar Iran Ali Akbar Salihi ya bayyana cewar mahalarta zaman taron sun cimma matsayar kafa kwamitin tuntuba da ya kunshi bangarori da dama na al'ummar Siriya domin shawo kan dukkanin bangarorin al'ummar Siriya musamman kungiyoyin da suka ki halartar zaman taron tattaunawar sulhun birnin Tehran, domin bunkasa zaman tattaunawan sulhu kan kasar ta Siriya. Salihi ya kara da cewar zaman taron tattaunawar sulhu kan kasar Siriya ya jaddada batun warware rikicin Siriya ta hanyar lumana kuma tsakanin al'ummar kasar ba tare da tsoma bakin kasashen waje ba tare da jaddada wajabcin ci gaba da kasancewar Siriya kasa daya dunkulalliya. Zaman taron ya kunshi wakilan jam'iyyun siyasa da kungiyoyi masu zaman kansu na ciki da wajen kasar Siriya 40, wakilan gwamnatin Siriya da na 'yan adawa, shugabannin kabilu da manyan mutane masu zaman kansu na ciki da wajen Siriya 130, wakilan addinai na Musulunci da na Kirista, baya ga wakilan gwamnatocin kasashe da na kungiyoyin kasa da kasa ciki har da na Majalisar Dinkin Duniya.
1139505