IQNA

Yan Gwagwarmayar Palasdinawa Suna Ci Gaba Da Kai Hare Haren Mai Da Martani.

16:17 - November 19, 2012
Lambar Labari: 2451301
'Yan gwagwarmayar Palasdinawa suna ci gaba da mai da martani kan hare haren wuce gona da irin sojojin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila ta hanyar harba makamai masu linzami kan manyan garuruwa da matsugunan yahudawan sahayoniyya 'yan kaka gida.
Breaking News
Yan Gwagwarmayar Palasdinawa Suna Ci Gaba Da Kai Hare Haren Mai Da Martani.Jirgin Saman Yakin H.K.Isra'ila Ya Yi Sanadiyyar Shahadar Palasdinawa Biyar.Ana Ci Gaba Da Kirga Kuri'un Zaben Da Aka Gudanar A Saliyo'Yan Bindiga Dadi Sun Harbe Wani Dan Majalisa A KanoPalastinawa Sun Ci Gaba Da Harba Makamai Masu Linzami Cikin HKIAdadin Palastinawan Da Suka Yi Shahada A Gaza Ya Kai Mutane 69Jiragen Yakin HKI Sun Kai Hare Hare Kan Ofishin Wani Gidan Television A Yankin GazaShugaban Nigeriya Ya Kore Batun Zaman Sulhu Da Kungiyar Boko Haram.Toron Tattaunawar Sulhu Kan Kasar Siriya A Birnin Tehran Na Kasar Iran Ya Kawo Karshen Zamansa. Kwamitin Tsaron M.D.Duniya Ya Yi Suka Kan 'Yan Tawayen DR Congo.Monday, 19 November 2012 06:56 Yan Gwagwarmayar Palasdinawa Suna Ci Gaba Da Kai Hare Haren Mai Da Martani.
font size decrease font size increase font size Print Add new comment

'Yan gwagwarmayar Palasdinawa sun harba makamai masu linzami fiye da dari kan manyan garuruwa da matsugunan yahudawan sahayoniyya 'yan kaka gida a rana ta biyar da kaddamar da hare haren wuce gona da iri kan yankin Zirin Gaza da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila ta yi, lamarin da ya tilastawa yahudawan sahayoniyya ci gaba da fakewa a maboyarsu ta karkashin kasa tare da dakatar da duk wata walwala a kan doron kasa. Har ila yau bangaren sojin Izzuddin Qassam na kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas ya dauki alhakin kakkabo jirgin saman yakin sojin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila kirar Hafaci. Haka zalika bangaren sojin na Izzuddin Qassam ya kai hare hare da makamai masu linzami kan jirgin ruwan yakin sojin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila, lamarin da ya tilastawa jirgin janyewa daga yankin da ya kafa tunga domin kai hare haren wuce gona da iri kan al'ummar Zirin Gaza.

1139614
captcha