IQNA

Hare Haren ta'addancin Wuce Gona Kan Al'ummar Gaza

15:47 - November 20, 2012
Lambar Labari: 2452039
Rahotannin da suke fitowa daga Zirin Gaza na nuni da cewa wasu Palastinawa 9 sun yi shahada, hudu daga cikinsu ‘yan gida guda a hare-hare na baya-bayan da sojojini HKI suke ci gaba da kai wa Gazan lamarin da ya kara adadin Palastinawan da suka yi shahada a Gazan zuwa mutane 110 mafiya yawansu kananan yara da mata da tsoffi sannan da wasu kuma sama da 900 da suka sami raunuka.

Rahotannin sun ce sojojin HKI sun kai hare-haren ta’addancin da suke ci gaba da kai wa al’ummar Gaza kimanin kwanaki shida da suka gabata ta sama da ta ruwa. Wata majiyar asibiti a Gaza ta bayyana cewar a hari na baya-bayan nan da sojojin yahudawan suka kai kan wani gida a kauyen Beit Lahiya da ke arewacin Gazan wasu mutane hudu ‘yan gida guda – wato mai gidan da mai dakinsa da kuma ‘ya’yansu biyu, daya dan watanni 18 daya kuma dan shekaru 4 sun yi shahada.

A bangare guda kuma kungiyoyin gwagwarmayar Palastinawan sun ci gaba da mayar da martani ta hanyar harba makamai masu linzami zuwa cikin garuruwa daban-daban na HKIn. Rahotanni sun ce ko a jiya kawai kungiyoyin gwagwarmayar Palastinawan sun sami nasarar harba makamai masu linzami sama da guda dari zuwa cikin HKI duk kuwa da ikirarin da yahudawan suke yi na cewa sun raunana karfin kungiyoyin gwagwarmayar.

Duk da irin takunkumin da sojoji da mahukuntan HKI suka sanya wa kafafen watsa labaransu dangane da fadin hakikanin abin da ke faruwa a can, amma dai ya zuwa yanzu rahotannin da suke fitowa daga can suna nuni da cewa adadin yahudawa ‘yan share guri zauna da suka halaka sakamakon hare-haren kungiyoyin gwagwarmayar Palastinawan sun kai 7 kana wasu kuma sama da 100 sun sami raunuka, duk kuwa da cewa akwai yiyuwar adadin ya fi haka.
1140361

captcha