Sayyid Nasrallah ya bayyana hakan ne a lokacin da yake gabatar da jawabi a wajen taron Ashura da kungiyar take shiryawa a birnin Beirut inda ya ce: HKI tana fatan ganin makaman kungiyoyin gwagwarmayar Palastinawa a Gaza sun kare ne don su ci gaba da danyen aikin da suke a can, don haka wajibi ne kasashen larabawa da na musulmi su bude kan iyakokinsu da kuma aikawa Palastinawan da makamai, kamar yadda kuma ya yi kakkausar suka ga kasashen larabawan da suke ba wa ‘yan adawar kasar Siriya makamai da kudaden amma kuma sun gaza wajen ba wa Palastinawan ko da harsashi guda don su yaki yahudawa ‘yan share guri zauna.
Har ila yau Sayyid Nasrallah ya jinjinawa Jamhuriyar Musulunci ta Iran da kuma kasar Siriya saboda gagarumin kokarin da suka yi wajen karfafa kungiyoyin gwagwarmayar Palastinawa ta hanyar ba su makaman da suke amfani da su a halin yanzu wajen kare kansu daga hare-haren ta’addancin HKI yana mai sake jaddada aniyar kasashen Iran da Siriya da kuma kungiyar Hizbullah din wajen ci gaba da goyon bayan al’ummar Palastinun.
1140308