Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci ta kasar Iran ya jaddada cewar Jamhuriyar Musulunci ta Iran tana alfahari tare da nuna jin dadi kan gabatar da taimako ta fuskar soji ga 'yan gwagwarmayar Palasdinawa da suke yankin Zirin Gaza. A jawabin da ya gabatar a gaban 'yan Majalisun Shawarar Musulunci na Iran bayan kammala zanga zangar da suka gudanar na yin Allah wadai da hare haren wuce gona da iri da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila ke kai wa kan yankin Zirin Gaza a yau Laraba: Ali Larijani ya jaddada cewar zanga zangar da muka gudanar a yau zanga zanga ce da ke bayyana cikekken goyon baya ga al'ummar Palasdinu da ake zalunta, kuma suke nuna gwarzontaka wajen kare kansu daga duk wani harin wuce gona da iri. Larijani ya kara da jaddada cewar Jamhuriyar Musulunci ta Iran zata ci gaba da kasancewa tare da al'ummar Palasdinu komai wahala har sai sun kai ga kwato dukkanin hakkokinsu. Har ila yau shugaban Majalisar Shawarar Musulunci ta Iran ya fayyace cewar gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila ta kaddamar da hare haren wuce gona da iri ne kan yankin Zirin Gaza da nufin neman ficewa daga halin kadaici da ta shiga a yankin gabas ta tsakiya, sai kuma ta kara afkawa cikin matsalar na kadaici tare da fuskantar Allah wadai.
1141890