A jiya da dare aka dakatar da bude wuta tskanin sojojin HKI da kuma dakarun kungiyar Hamas da Jihadul Islami a yankin gaza. Dakatar da bude wutan wanda ya fara da misalin karfe 07 agogon GMT ya kawo karshen yakin kwanaki 8 wanda sojojin HKI suka soma shi da kashe daya daga cikin shuwagabannin dakarun hamas a yankin Gaza Ahmad Al-jabiri a ranar laraban ta sama. Palasdinawa kimani 160 ne suka yi shahada a yayinda wasu fiye da dubu daya suka ji raunuka a hare haren da sojojin yahudawan suka yi ta kaiwa a kan yankin na gaza na tsawon wadan nan kwanaki. A maida martani da dakarun kungiyoyin Hamas da kuma jihadul Islami suka yi a cikin wadannan kwanaki, ya halaka yahudawa da dama ya kuma raunata wasu. A karon farko, a wannan yakin makaman linzami wadanda kungiyoyin Palasdinawa a yankin na gaza suka yi ta cillawa kan HKI, sun kai birnin Telabiv sun kuma halaka yahudawa da dama. Wadan nan makaman ne suka tilastawa HKI amincewa da dakatar da bude wuta a jiya da dare, tare da sharuddan da wadanna kungiyoyo biyu suka shimfida mata. A cikin yerjajniyar tsagaita bude wutan da bangarorin biyu suka cimma dai a kwai batun dage kofar ragon da aka yiwa yankin na gaza fiye da shekaru 5 da suka gabata. Wanda kuma zai fara sa'oi 24 bayan dakatar da bude wuta. 1142087