Bangaren kasa da kasa; Ayatullahi Isa Kasim limamin masallacin juma'a a birnin Manama fadar mulkin kasa Bahrain a ranar sha bakwai ga watan Azar na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in da daya hijira kamariya a cikin khudubar sallar juma'a ya yi Allah wadai da yadda sojojin Ali Khalifa sarkin wannan kasar ke ci gaba da rusa masallatai gurin ibadar musulmi.
Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin da suka shafi kur'ani mai girma a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: Ayatullahi Isa Kasim limamin masallacin juma'a a birnin Manama fadar mulkin kasa Bahrain a ranar sha bakwai ga watan Azar na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in da daya hijira kamariya a cikin khudubar sallar juma'a ya yi Allah wadai da yadda sojojin Ali Khalifa sarkin wannan kasar ke ci gaba da rusa masallatai gurin ibadar musulmi. Ya gabatar da sallar juma'ar ne a masallacin Imam Sadik (AS) da ke yankin Diraz na birnin Manama fadar mulkin kasar Bahrain inda ya kara da cewa; a yau mun sake ganin yadda gwamnatin wannan kasa ta sake daukan mataki na rusa masallatai da guraren ibadar musulmi kuma wannan shi ne cin mutunctu da rashin girmama guraren ibadar musulmi da addinin musulunci. Gwamnatin Bahrain dai ta yi fice wajan kisan gilla kan musulmi musamman masu nuna adawarsu da salon mulkin gidan sarautar Ali Khalifa wanda yayi kunnan uwar shegu kan sauraren koken talakkawan wannan kasa.
1149337