IQNA

Makiya HKI Ne Za Su Amfana Da Duk Wata Fitina A Tsakanin Musulmi

16:06 - December 08, 2012
Lambar Labari: 2460025
Bnagren kasa da kasa; babban sakataren kungiyar gwagwarmaya ta Hizbullahi a kasar Labanon ya jaddada cewa: duk wata fitina da za ta wakana a tsakanin musulmi zai amfani makiyan musulmi haramtacciyar kasar Isra'ila don haka ana bukatar kawokarshen duk wasu maganganu da hudubobi da za su kawo Baraka da rarrabuwar kawuna a tsakanin musulmi kuma a fadada jawabai da maganganu da za su kara kusanci da hadin kai a tsakanin musulmi.



Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin da suka shafi kur'ani mai girma a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: babban sakataren kungiyar gwagwarmaya ta Hizbullahi a kasar Labanon ya jaddada cewa: duk wata fitina da za ta wakana a tsakanin musulmi zai amfani makiyan musulmi haramtacciyar kasar Isra'ila don haka ana bukatar kawokarshen duk wasu maganganu da hudubobi da za su kawo Baraka da rarrabuwar kawuna a tsakanin musulmi kuma a fadada jawabai da maganganu da za su kara kusanci da hadin kai a tsakanin musulmi.Said Hasan Nasrullah babban sakataren kungiyar gwagwarmyata ta Hizbullahi a kasar labanon a lokacin da yake bayani a gaban daruruwan dalibai inda ya bukaci musulmin duniya kan su yi hattara da duk wani abu da zai kawo Baraka a tsakanin musulmi da kuma irin hadarin da ke tattare da rikicin addini a tsakanin musulmi da la'akari da wanda zai cimma nasara kan haka wato haramtacciyar kasar Isra'ila.
1149378

captcha