IQNA

An Fara Gudanar Da Taron Malaman Jami'oi Da Farkawa Ta Musulunci

12:46 - December 11, 2012
Lambar Labari: 2461896
Shugaban kasar Dakta Mahmud Ahmadinejad ya bayyana cewar farkawa ta Musulunci ba lamari ne da ya takaita ga musulmi kawai ba face dai dukkanin bil’adama suna fatan ganin an tabbatar da adalci da kuma ‘yanci ga kowa.
Shugaban na Iran ya bayyana hakan ne a lokacin da ya ke gabatar da jawabinsa a wajen taron kasa da kasa na malaman jami’oi da kuma farkawa ta Musulunci inda ya ce a daidai lokacin da ake tunani kan halin da Palastinawa suke ciki sakamakon irin mamayan da yahudawa suke musu, wajibi ne kuma a dinga tunani kan matsalolin da wasu mutanen suke ciki a kasashen Afirka, Amurka da sauran yankuna na duniya.



Shi ma a nasa bangaren babban sakataren taron farkawa ta Musulunci Dakta Ali Akbar Wilayati ya jinjinawa irin nasarar da al’ummar Gaza suka samu a kan yahudawa ‘yan share guri zauna cikin yakin kwanaki takwas da HKI ta kaddamar a Gaza inda ya ce hakan daya ne daga cikin sakamako na farkawa ta Musulunci da al’umma suka samu.



A yau ne dai aka bude wannan taron na kwanaki biyu wanda ya sami halartar masana da malaman jami’oi kimanin 350 daga ciki da wajen kasar Iran.


1150930
captcha