A lokacin da ya ke gabatar da jawabin bude taron, shugaban kasar Iran Dakta Mahmud Ahmadinejad ya yi ishara da irin rawar da malaman jami’a da sauran masana za su taka wajen kyautata rayuwar al’ummar su. Har ila yau kuma yayin da yake magana kan ma’anar farkawa ta Musulunci, shugaba Ahmadinejad ya bayyana cewar hakan yana nufin komawar bil’adama ne zuwa ga hakikanin yanayinsu na ‘yan’adam.
Shi ma a nasa bangaren babban sakataren cibiyar kasa da kasa ta farkawa ta Musuluncin Dakta Ali Akbar Wilayati ya bayyana cewar farkawa ta Musulunci da aka samu a kasashen musulmi tana a matakinta na farko ne don haka akwai bukatar aiki tukuru wajen cimma manufofin da aka sanya a gaba.
Har ila yau a ranar farko na wannan taron, malaman jami’oi da sauran masana mahalarta taron sun gudanar da jawabansu da kuma bayyanar da mahangarsu kan wannan batu na farkawa ta Musulunci.
A rana ta biyu ta taron, mahalarta taron sun kai ziyarar ban girma wa Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei inda ya jagoran ya yi karin haske kan ma’anar farkawa ta Musulunci da kuma batutuwa daban-daban da suka shafi kasashen musulmi.
A jawabin da ya gabatar yayin wannan ganawar Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya bayyana cewa babban abin da yake daga hankalin makiya Musulunci a halin yanzu shi ne farkawar al’ummar musulmi a duniya. Jagoran ya kara da cewa makiya Musulunci suna tsoron farkawa ta hakika tsakanin musulmi, domin kuwa hakan ne zai sanya musulmi su gane makiyansu na hakika, duk kuwa da cewa makiya Musulunci ba su tsoron da dama daga cikin shugabanni ko sarakuna na kasashen musulmi, saboda su ba barazana ba ne a wurinsu ba, kai bilhasali ma da dama daga cikinsu ‘yan amshin shatan makiya musuluncin ne.
A ranar karshe na taron dai bayan wasu daga cikin mahalarta taron sun gabatar da jawabansu, da kuma gama ayyukan kwamitocin da aka kafa, mahalarta taron sun fitar da takardar bayan taro da ta kumshi batutuwa da dama da suka hada da kira da a karfafa irin farkawar da al’ummar musulmi suka yi a kasashe daban-daban kamar yadda kuma suka bayyanar da goyon bayansu ga al’ummar Palastinu a gwagwarmayar da suke yi na kwato hakkokinsu da yahudawa ‘yan share guri zauna suke ci gaba da takewa. Har ila yau mahalarta taron sun yi kiran da a tabbatar da hadin kai da aiki tare tsakanin kasashe da al’ummar musulmi kamar yadda kuma suka yi kiran da a samar da yanayin musayen ilimi da kwarewa tsakanin kasashen musulmi.
Wannan taro na kwanaki biyu dai ya sami halartar malaman jami’oi da masana daga kasashe kimanin 71 na duniya