IQNA

Masu Goyon Bayan Kundin Tsarin Mulkin Masar Su Ne A Kan Gaba

14:14 - December 16, 2012
Lambar Labari: 2464726
A kasar Masar ana ci gaba da kidayen kuri’un da al’ummar kasar suka kada a kuri’ar jin ra’ayin al’ummar kasar zagaye na farko da aka gudanar a jiya asabar a daidai lokacin da masu goyon baya da kuma adawa da kundin tsarin mulkin suke ci gaba da tuhumar junansu da aikata ba daidai ba.




Sakamakon farko-farko da wasu kafafen watsa labarai da kuma wasu majiyoyi suka fitar suna nuni da cewa masu goyon bayan kundin tsarin mulkin su ne suke a kan gaba a yankuna daban-daban da aka gudanar da kuri’ar jin ra’ayin al’ummar. Wasu rahotannin ma suna cewa nasarar da masu goyon bayan kundin tsarin mulkin suka samu ya kai kashi 65%, duk da cewa za a sanar da asalin sakamakon kuri’ar ne a hukumance bayan an gudanar da zagaye na biyu na kuri’ar da za a gudanar a ranar asabar mai zuwa.

To sai dai kuma a daidai lokacin da ake ci gaba da kidayar kuri’ar, masu adawa da kundin tsarin mulkin sun zargi kungiyar Ikhwan al-Musulmin wadda shugaban kasar Masar din Muhammad Morsi ya fito daga cikinta da kokarin magudin zabe, a daidai lokacin da ‘yan Ikhwan din kuma suke zargin ‘yan adawar da amfani da kudi da kuma hanyoyi na karya wajen shafa kashin kaji ga kundin tsarin mulkin.

A jiya ne dai al’ummar Masar din suka fito don kada kuri’arsu kan sabon kundin tsarin mulkin kasar wanda ya janyo kace-nace da rikici a kasar. Rahotanni dai sun ce al’umma sun fito ainun lamarin da ya sanya aka kara sa’oin kada kuri’ar don ba da dama wa mutane kada kuri’arsu.


1154220
captcha