Bangaren siyasa:Ramin Mehman Perast kakakin ma'aikatar harkokin wajen jamhuriyar musulunci ta Iran ya nuna takaici da mamaki da yadda ministan harkokin wajen kasar Britaniya ke coba baki da yin shiga shigula a cikin harkokin cikin gida na jamhuriyar musulunci ta Iran tare da yin Allah wadai kan wannan hali na rashin mutunta dokokin kasa da kasa da kuma dokoki da hakkokin sauran kasashe.
Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin da suka shafi harkokin kur'ani mai girma a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ya watsa rahoton cewa: Ramin Mehman Perast kakakin ma'aikatar harkokin wajen jamhuriyar musulunci ta Iran ya nuna takaici da mamaki da yadda ministan harkokin wajen kasar Britaniya ke coba baki da yin shiga shigula a cikin harkokin cikin gida na jamhuriyar musulunci ta Iran tare da yin Allah wadai kan wannan hali na rashin mutunta dokokin kasa da kasa da kuma dokoki da hakkokin sauran kasashe. Yadda ministan harkokin wajen kasar ta Britaniya ke coma baki a cikin harkokin cikin gida na jamhuriyar musulunci ta Iran abin mamaki ne a daidai lokaci da gwamnatin Britaniya ke zargin wasu da coma baki a cikin harkokin wasu kasashe kuma abin yin Allah wadai ne.
1159513