IQNA

Shirin Arba'in Huseini A Karbala

15:47 - December 27, 2012
Lambar Labari: 2471047
Shugaban kwamitin tsaro na majalisar lardin Karbala a kasar Iraki ya sanar da cewa jami’an tsaron lardin sun sami nasarar kame wasu ‘yan ta’adda da suke shirin kai hari garin a lokacin juyayin arba’in na Imam Husain (a.s) da za a gabatar a garin a mako mai zuwa.
Kamfanin dillancin labaran Aswat al-Iraq ya jiyo Hamid Sahib Shugaban kwamitin tsaro na majalisar lardin Karbalan yana cewa jami’an tsaron sun sami nasarar kame wadannan ‘yan ta’adda su hudu ne da suke shirin kai harin ranar arba’in sannan kuma ana ci gaba da gudanar da bincike a kansu don gano daga wace kungiya suke da kuma sauran bayanai dangane da wannan mugun nufi na su.

A farko-farkon wannan makon ma dai jami’an tsaron kasar Irakin sun cafke wasu ‘yan ta’addan a kokarin da suke yi na shigar da makamai da wasu bama-bamai zuwa garin na Karbala da nufin amfani da su a ranar arba’in din.

Ya zuwa yanzu dai jami’an tsaron kasar sun sanar da daukan tsauraran matakan tsaro a duk fadin lardin da nufin tabbatar da tsaro da zaman lafiyan miliyoyi mabiya Ahlulbaiti (a.s) da za su kai ziyara garin na Karbala don halartar bukukuwan juyayin ranar arba’in din duk kuwa da kokarin da wasu makiya suke yi na ganin hakan ba ta tabbata ba.

1160943
captcha