IQNA

Maida Martani Da Ma'aikatar Harkokin Waje Ta Maida

15:46 - December 27, 2012
Lambar Labari: 2471048
Sojojin ruwa na Jamhuriyar Musulunci ta Iran sun sami nasarar kera wata na’ura mai harba makamai masu linzami da kuma ba da kariya ta zamani wacce za ta kara irin karfi da kuma shirin da sojojin suke da shi wajen kare kasar daga duk wani shirin wuce gona da iri na makiya.

Yayin da ya ke sanar da wannan labarin, babban hafsan hafsoshin sojojin na Iran Rear Admiral Habibullah Sayyari ya ce za a iya kafa wannan sabuwar na’urar a kan dukkanin jiragen yaki na ruwa sannan kuma nan ba da jimawa ba za a mika ta ga dakarun ruwan don fara amfani da ita.

Kamfanin dillancin labaran Fars na Iran ya bayyana cewar dakarun sojin ruwan na Iran da hadin gwuiwan ma’aikatar kera makamai da kuma jami’ar sojin ruwa ta Imam Khumaini (r.a.) da ke garin Bushehr ne suka kera wannan sabuwar na’urar.

Bisa la’akari da irin karfin da Iran take da shi a fagen makamai masu linzami, don haka ana ganin sake kera wannan na’urar a matsayin wata sabuwar nasara da Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta samu a fagen kare kanta musamman a wannan lokacin da makiyanta suke ci gaba da yi mata barazanar kawo mata hari.

1161032
captcha