IQNA

Maida Martani Da Ma'aikatar Harkokin Waje Ta Maida kan Kasar Britaniya

15:53 - December 27, 2012
Lambar Labari: 2471054
ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran, ta bakin mai magana da yawun ma’aikatar Ramin Mehmanparast, ta yi Allah wadai da maganganun da sakataren harkokin wajen Birtaniyya William Hague ya yi dangane da yanayin wasu masu laifi da aka yanke musu hukumci a Iran, inda ma’aikatar tace akwai wata manufa cikin wannan bayani nasa.

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen na Iran, wanda ya ke ganawa da manema labarai a ranar lahadin da ta gabata ya ce abin da ministan na Birtaniya ya fadi ya saba wa hakikanin abin da ke faruwa a Iran yana mai cewa hakan ci gaba ne na kokarin da jami’an Birtaniyan suke yi wajen fakewa da batun kare hakkokin bil’adama don cimma bakaken manufofinsu a kan Iran.

Ramin Mehmanparast ya ci gaba da cewa: kasar Birtaniya wacce take da bakin tarihi na mulkin mallaka da kuma take hakkokin bil’adama, ba ta da bakin magana cikin batun kare hakkokin bil’adama a duniya.

Sakataren harkokin wajen Birtaniyan William Hague ya yi wadannan kalamai nasa ne a ranar alhamis din da ta gabata a lokacin da yake magana kan wani kuduri da babban zauren MDD ya fitar wanda kuma kasar Kanada ta gabatar masa kan batun hakkokin bil’adama a Iran.

1160507
captcha