IQNA

Bincike kan Falsafar Shahadar Imam Huseini (AS)

16:03 - January 02, 2013
Lambar Labari: 2474700
Bangaren kasa da kasa: a wani taro da aka gudanar a babban birnin kasar faransa Paris a daidai wannan lokaci na kusancin ranar Arba'in da tunanawa da shahadar imam Huseini (AS) za a gudanar da bincike kan falsafar Shahadar Imam Huseini (AS).


Kamfanin dillancin labarai na Iqna da ke kula da harkokin kur'ani mai tsarki a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton ce: : a wani taro da aka gudanar a babban birnin kasar faransa Paris a daidai wannan lokaci na kusancin ranar Arba'in da tunanawa da shahadar imam Huseini (AS) za a gudanar da bincike kan falsafar Shahadar Imam Huseini (AS). A ranar juma'a mai zuwa sha biyar ga watan nan da muke ciki na hijira shamsiya ta dubu daya da dari uku da tis'in da daya wadda ta yi daidai da ranar hudu ga watan janairun sabuwar shekara ta dubu biyu da goma sha uku masana da malamai na addini da masu bincike da nazari za su gudanar da wani taron bincike da nazari a ofishin da ke kula da yada al'adun jamhuriyar musulunci ta Iran a kasar Faransa kan falsafar da ke tattare da shahadar Imam Huseini (AS) kuma za su fara wannan taro ne da misalign karfe biyar na rabi na marece agogon wannan kasa.

1164616
captcha