IQNA

An Kwalaye dari biyu na Magunguna ga Masu Ziyarar Arba'in Ta Husein

16:02 - January 02, 2013
Lambar Labari: 2474701
Bangaren kiwon lafiya: shugaban cibiyar da ke kula da likitoci masu kula da mahajjata da masu ziyara na Hilalul ahmar ya bayyana cewa: a daidai wannan lokaci da gudanar da tarorrukan arba'in na juyayin shahadar imam Huseini (AS) a karbala na kasar Iraki sun aike da kwalaye dari biyu da suka kumshi magunguna da abubuwa na kiwon lafiya ga masu ziyarar a wannan yanki wadanda ba Iraniyawa ba a wannan shekara.



Kamfanin dillancin labarai na Iqna da ke kula da harkokin kur'ani mai tsarki a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton ce: shugaban cibiyar da ke kula da likitoci masu kula da mahajjata da masu ziyara na Hilalul ahmar ya bayyana cewa: a daidai wannan lokaci da gudanar da tarorrukan arba'in na juyayin shahadar imam Huseini (AS) a karbala na kasar Iraki sun aike da kwalaye dari biyu da suka kumshi magunguna da abubuwa na kiwon lafiya ga masu ziyarar a wannan yanki wadanda ba Iraniyawa ba a wannan shekara. Said Ali Riyad shugaban shugaban cibiyar da ke kula da harkokin da suka shafi kiwon lafiyar maniyata da maziyarta a nan Iran yay i bayani dalla dalla kan ayyukan da suke gudanarwa a guraren ayyukan addini da gurare na ziyara da kuma irin gudummuwa da irin taimakon da jamhuriyar musulunci ta Iran karkashin wannan cibiya ta su ta hilalun Ahmar ke gudanarwa a ci da wajen Iran.

1164605
captcha