A safiyar yau talata (8-1-2013) ne Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya gana da dubun dubatan mutanen birnin Qum don tunawa da zagayowar shekarar yunkurin 19 ga watan Dey na al'ummar Qum din. A lokacin da yake gabatar da jawabi a wajen ganawar, Jagoran ya bayyana wannan yunkuri na 19 ga watan Dey na mutanen Qum a matsayin wani abu da ke tabbatar da gaskiyar alkawarin Ubangiji sannan kuma yayin da yake jaddada muhimmancin tsayin daka da taka tsantsan wajen fuskantar makirce-makircen makiya musamman a lokacin zaben shugaban kasa da za a gudanar a nan gaba, Jagoran ya yi ishara da wasu batutuwa masu muhimmanci dangane da nauyin da ke wuyan jami'an, zababbun cikin al'umma, kafafen watsa labarai da kuma wadanda suke da niyyar tsayawa takaran zaben.
Ayatullah Khamenei ya bayyana yin tunani da kuma dubi cikin abubuwan da suka faru a lokacin juyin juya halin Musulunci da kuma tsawon shekaru talatin da wani abu da nasarar juyin juya halin Musulunci, bugu da kari kan daukan darussa cikin wadannan abubuwan da suka faru irin su wannan yunkuri na 19 ga watan Dey a matsayin wani lamari da ya zama wajibi, daga nan kuma sai ya ce: Wasu suna ganin samun nasarar al'umma a kan gwamnatin dagutu da kuma fitar da Iran daga cikin wulakanci na ikon Amurka a matsayin wani lamari da ba zai yiyu ba, to amma da taimakon Allah an yi watsi da wancan gwamnati ta gidan sarauta cikin kwandon sharar tarihi sannan kuma Jamhuriyar Musulunci da kuma al'ummar Iran sun sami cikakken 'yancinsu a gaban Amurka.
Jagoran ya bayyana irin nasarori da Iran ta dinga samu tsawon wadannan shekaru talatin na baya-bayan nan a matsayin abin da ke tabbatar da alkawari da kuma taimakon Ubangiji, sannan kuma yayin da yake ishara da wasu ayoyi daban-daban na Alkur'ani mai girma, Jagoran ya bayyana cewar: Ko shakka babu muminai sannan kuma ma'abota taka tsantsan da tsayin daka za su sami taimakon Allah a lokacin da ya dace, hakan kuwa wata sunna ce ta Ubangiji da ba za a taba sauya ta ba. Bisa wannan sunna ce ya sanya al'ummar Iran a wannan yanayin da kuma sauran lokuta na daban za su yi nasara a kan makiyansu.
Haka nan kuma yayin da yake ishara da wajibcin gabatar da ingantacciyar manufa da kuma mahangar al'ummar Iran ga sauran al'ummomin duniya don ciyar da manyan manufofinsu gaba, Jagoran juyin juya halin Musuluncin cewa ya yi: Matukar dai al'ummar Iran masu girma da kuma matasansu masu kumaji suka ci gaba da riko da wannan tafarki da suke kai, to ko shakka babu haka nan kuma bisa sunna ta Ubangiji sannan kuma a lokacin da ya dace za su cimma dukkanin fatan da taken na kasa da na musulunci da na duniya da suke da su. Za a sauya tafarkin tarihi da kuma share fagen bayyanar mai girma Imam Mahdi (Allah ya gaggauta bayyanarsa).
Har ila yau kuma Ayatullah Khamenei ya yi ishara da irin yadda ma'abota girman kai suka hada kai da juna wajen sanya wa Iran takunkumi da kuma irin tsayin dakan da al'ummar Iran suka yi wajen fuskantar wannan takunkumin inda ya ce: Sabanin shekarun baya a halin yanzu ma'abota girman kai a fili suke fadin cewa manufar wadannan takunkumin ita ce gajiyar da al'ummar Iran don su yi fito na fito da tsarin Jamhuriyar Musulunci da kuma matsa wa jami'ai lamba, don hakan ya tilasta musu sauya matsayarsu.
Jagoran ya ci gaba da cewa: To amma rikon da wannan al'umma mai girma ta Iran ta yi ga koyarwar Musulunci da juyin juya hali da kuma daukaka ta kasa a kowace rana sai dada karuwa suke yi. Hakan kuwa sabanin abin da makiyan suke so ne.
Haka nan kuma yayin da yake sharhi kan abubuwan masu tasiri cikin fadar da gwamnatocin ma'abota girma kai suke yi da al'ummar Iran, Jagoran ya bayyana yin taka tsantsan a matsayin wani wajibi da ke kan al'ummar Iran, daga nan sai ya ce: Wajibi ne su fahimci irin makirce-makircen makiya ta hanyar yin taka tsantsan da nuna sanin ya kamata na gaba daya na al'umma, sannan kuma kada mu bari wani abu ya kawar da hankulanmu daga makiyan.
Jagoran juyin juya halin Musulunci ya sake jaddada kiraye-kirayen da ya saba yi wa jami'an gwamnati da kafafen watsa labarai da shafuffukan internet na su guji shagaltar da mutane da abubuwa na bayan fage inda ya ce: Ina yin dukkanin wadannan kiraye-kirayen ne saboda su tattaro hankulanmu waje guda da fahimtar manufar da makiya suke son cimmawa.
Ayatullah Khamenei ya ci gaba da cewa: Dubi cikin halaye da maganganun ma'abota girman kai yana nuni da cewa makiya sun sanya dukkanin idanuwa da tunaninsu ne kan zaben (shugaban kasa) da za a gudanar nan da watanni biyar masu zuwa, wato a watan Khordad na shekarar 1392.
Jagoran ya ci gaba da Karin haske kan hanyoyin da makiyan suke bi wajen yin tasiri a cikin zaben shugaban kasar da za a yi a Iran inda ya ce: Abu na farko da suke son cimmawa shi ne su hana a gudanar da zaben, to amma sun san cewa ba za su iya ba, don haka suka yanke kauna.
Daga nan Jagoran ya ci gaba da cewa: A wani lokaci a baya wasu sun so a jinkirta zaben ko da na mako biyu ne, to amma mu dai mun tsaya kyam kan cewa bai kamata a jinkirta gudanar da zaben ba ko da na rana guda ne. A saboda haka ne ya zamana an rufe kofar jinkirta gudanar da zaben ko kuma a ki gudanar da shi.
Ayatullah Khamenei ya bayyana kokarin yin tasiri da hana mutane fitowa zaben a matsayin wata manufar da makiyan suka sa a gaba, inda ya ce: Wajibi ne kowa da kowa ya yi taka tsantsan, kai hatta ma mutanen da mai yiyuwa ne su fadi wasu kalmomi da za su kashe wa mutane gwiwa su yi taka tsantsan kada su taimaka wa makiya a wannan fagen.
Haka nan kuma yayin da ya ke sukan wasu mutane da suke ci gaba da nanata batun cewa wajibi ne zaben ya kasance cikin 'yanci, Jagoran cewa ya yi: Na'am a fili yake cewa wajibi ne a gudanar da zabe cikin 'yanci, to amma shin akwai wani lokaci ne cikin wadannan shekaru talatin din da aka taba gudanar da zaben ba cikin 'yanci ba? Wace kasa ce zabenta ya fi na Iran zama cikin 'yanci? Lalle ku yi hankali da irin wadannan maganganu da kuke fadi don kada ku kashe wa mutane gwiwa.
Har ila yau Ayatullah Khamenei ya ci gaba da karin haske kan hanyoyin da za su iya taimakawa makiya cimma manufar da suke son cimmawa a lokacin wannan zaben inda ya ce: A wace kasa ce ba a lura da wasu dokoki wajen tace 'yan takara? Don me ya sa kuke ta magana kan wannan lamarin don ku sanya wa mutane jin cewa babu wani amfanin kada kuri'a a lokacin zaben?
Jagoran ya ja kunnen mutanen da suke irin wannan aikin ko sun sani ko ba su sani bad a cewa: Bai kamata ku gafala ba, sannan ku cika wa makiya burin da suke das hi.
Har ila yau Jagoran ya yi kakkausar suka ga mutanen da suke kokarin wajen nuna wa mutane cewa zaben ma ba shi da wani inganci da ake bukata, inda ya ce hakan daya ne daga cikin hanyoyin da za su kai makiya ga cimma manufar da suka sa a gaba
Jagoran juyin juya halin Musulunci ya ci gaba da cewa: Tabbas ni din nan ina jaddada cewa wajibi ne zabe ya zamanto ingantacce sannan kuma cikin gaskiya da rikon amana sannan kuma ina kiran dukkanin jami'an gwamnati da ma wadanda ba na gwamnati ba wajen kiyaye dokoki don a sami gudanar da ingantaccen zabe, kuma ina da yakinin hakan ne zai faru.
Har ila yau kuma Ayatullah Khamenei ya jinjinawa hanyoyi da kuma dokokin da aka kafa wajen tabbatar da cewa an gudanar da ingantaccen zabe inda ya ce: Riko da dukkanin wadannan hanyoyi da dokoki lamari ne da zai tabbatar da gudanar da ingantaccen zabe, sai dai idan har wasu suna son su gudanar da wasu abubuwan da suka saba wa doka, kamar yadda wasu suka yi a lokacin zaben shugaban kasar da aka gudanar a shekara ta 2009 da kuma haifar da fitina a kasar nan.
Haka nan kuma yayin da yake ishara da fatan da makiya suke da shi wajen ganin al'umma ba su fito a lokacin zaben ba, Jagoran juyin juya halin Musuluncin cewa ya yi: Mai yiyuwa ne a ranakun zaben wasu su yi kokari kokarin wajen shagaltar da mutane da batutuwa irin na tattalin arziki da siyasa ko tsaro da sauransu, wanda hakan yana daga cikin makirce-makircen makiya. Ko da yake tabbas na san al'ummar Iran sun fi karfin a yi wasa da hankulansu da wadannan makirce-makirce na makiya ko kuma 'yan amshin shatansu.
A ci gaba da jawabin nasa, Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya yi ishara da wasu batutuwa da suka shafi su kansu 'yan takaran da za su fito a zaben shugaban kasar da za a gudanar inda ya bayyana cewar shigowa cikin zabe wani hakki ne da kuma nauyi da ke a wuya, don haka sai ya ce: Daidaikun mutanen da suka yarda da tsarin Jamhuriyar Musulunci da kuma kundin tsarin mulki suna da hakkin amfani da hakkin da suke das hi, wasu kuma daga cikinsu suna son su gabatar da irin dacewa da kuma kwarewar da suke da ita wa al'umma.
Jagoran juyin juya halin Musulunci ya kara da cewa: Aikin gudanar da kasa ba karamin aiki ba ne, face dai aiki ne mai nauyin gaske a wuyan manyan jami'an gudanarwa na gwamnati. A saboda haka kamata ya yi mutanen da suke da irin wannan karfi sannan suke jin cewa lalle suna da shi ne ya kamata su tsaya takaran.
Jagoran ya ci gaba da cewa: Mai yiyuwa ne wani yana gudanar da aikinsa ne a wani bangaren, daga baya ne zai fahimci cewa lalle aikin gudanar da wata kasa ba karamin aiki ba ne. A saboda kamata ya yi mutanen da suke ganin suna da kwarewa a wannan fagen ne za su yi rajistar sunayensu.
Jagoran ya ci gaba da cewa: Wajibi ne 'yan takaran shugabancin kasa su zamanto masu riko da kuma biyayya ga wannan tsarin da kuma kundin tsarin mulki na kasa, sannan kuma a hakikanin gaskiya suna son su aiwatar da kundin tsarin mulkin ne, don kuwa shugaban kasa yana rantsuwa ne da cewa zai kare kundin tsarin mulki, sannan kuma bai kamata ya yi rantsuwa kan karya ba.
A karshen jawabin nasa kan batun zaben, Ayatullah Khamenei cewa ya yi: Da yardar Allah, za a gudanar da gagarumin zabe kuma mai kyaun gaske a watan Khordad na shekara mai zuwa ta 1392.
1168349