IQNA

Babban Sakataren Kungiyar Hizbullah Zai Yi Jawabi Kan Makon Hadin Kai

23:22 - January 23, 2013
Lambar Labari: 2485449
Bangaren kasa da kasa, babban sakataren kungiyar gwagwarmaya ta hizbullah a kasar Lebanon Sayyid Hassan Nasrullah zai gabatar da jawabi kan makon hadin kai wada kafofin yada labarai za su watsa kai daga birnin Beirut na kasar Lebanon kamar dai yadda bayanin kungiyar ta ya tabbatar.

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar talabijin din Alamanr cewa, babban sakataren kungiyar gwagwarmaya ta hizbullah a kasar Lebanon Sayyid Hassan Nasrullah zai gabatar da jawabi kan makon hadin kai wada kafofin yada labarai za su watsa kai daga birnin Beirut na kasar Lebanon, inda zai tabo muhimman batuwa da suka shafi duniyar musulmi a yau.

Sanarwar t ace a cikin baynain nasa Sayyid Nasrullah zai tabo halin da ake ciki a yankin gabas ta tsakiya, da kuma irin makircin da makiya msulunci suke kullawa ma larabawa da musulmi ta hanyar yin amfani da wasu daga cikin karnukan farautar kasashen yammacin turai da suke mulkin kasashen musulmi da na larabawa.

Sayyid Nasrullah dai na daya daga cikin muhimman mutane da suka tsonewa haramtacciyar kasar Isra'ila ido, kuma take fatan ganin bayansu ko taw ace hanya, kuma take daukar matakai na leken asirin ta hanaar wasu daga cikin munafukai a kasar ta Lebanon, lamarin day a sanya shi buya daga idanun muatane, inda yak an gabatar da jawabansa kai tsaye ta manyan allunan talabijin ga al'ummar kasar da ma sauran musulmi.

1176410


captcha