IQNA

23:26 - January 25, 2013
Lambar Labari: 2485802

Shugaban kasar Syria Bassharul-Assada ya halarci taron maulidin ma'aiki (s.a.wa.)

Bangaren kasa da kasa, shugaban Syria Bashar Assad ya halarci taron maulidin manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata gare shi da iyalan gidansa tsaraka a birnin Damascus tare da halartar malaman addini da kuma masana daga ssa daban-daban na kasar, gami da malaman jami'oi.



Kamfanin dilalncin labaran iqna ya nakalto daga tashr Al-ikhbariyya cewa, shugaban kasar Syria Bassharul-Assada ya halarci taron maulidin ma'aiki (s.a.wa.) dazu a birnin Damascuss. Tashar telbijin din gwamnatin Syria ta nuna hotunan shugaba Basshar Asad a daya daga cikin masallatan birnin Damascuss da ake gabatar da bikin maulidin manzon Allah (s.a.wa.) a tare da muffin kasar Ahmad Badruddin Hassun da pira minister Wa'il al-halqy da kuma ministan mai kula da harkokin addini Muhammad Abdul-Sattar al-Sayyid da kuma wasu manyan jami'an gwamnati. Ministan harkokin addini na kasar ya jaddada kiran da shugaban kasar ya yi a jawabinsa na karshe a farkon wannan watan na janairu da bude tattaunawa a tsakanin dukkanin al'ummar kasar kowace irin akida ta siyasa su ke riko da ita." A ranar 6 ga watan Janairu da ake ciki ne shugaba Basshar Asad ya gabatar da jawabi a wani dakin taro da ke tsakiyar birnin Damascuss da a ciki ya yi kira bude tattaunawa tsakanin dukkanin bangarorin kasar domin tabbatar da hadin kan Syria.

1177273






























captcha