Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa cewa baya da lamurra suka cakude a kasar Masar sakamakona bubuwan da suka biyu bayan tarukan cika shekaru biyu da samun nasara juyi a kasar babbar jamia'r muslunci ta kasar Masar ta nuna shawar shigga tsakanin bangarorin da ke rikici domin akucewa fadawa cikin wani abu na daban a kasar wadda ked a mabanbanta ra'ayoyi.
Babbar gamayyar jam'iyyun adawa a kasar Masar ta nuna cikakken goyon bayanta ga masu zanga-zanga a kasar da ke neman a kifar da gwamnatin Muhammad Mursi, bisa zarginsa da kisan fararen hula masu zanga-zanga a kasar da ba su gamsu da salon mukinsa ba.
A cikin bayanin da gayammar jamiyun adawar na kasar Masar ta fitar a yau, ta zargi Muhammad Mursi da yunkurin mayar da kasar Masar bisa turba da tunani na kungiyar 'yan uwa musulmi, alahali kuwa a cewar bayanin an zabi Mursi ne da sunan demokradiyya bayan kawar da tsarin zalunci da fir'ananci na Husni Mubarak.
Bayanin ya ce gamayyar jamiyun adawar kasar Masar na goyon bayan abin da masu zanga-zanga suke kira na a gurfanar da Muhammad Mursia agaban kuliya domin hukunta kan kisan masu zanga-zanga tare da duk wadanda suke da hannu wajen bayar da umuri ko aiwatar da hakan kan fararen hula.
Tun daga ranar Juma'ar da ta gabata 25 ga watan Janairu wanda ya yi daidai da ranar da ake cika shekaru biyu da faduwar gwamnatin Husni Mubarak, kasar ta Masar take ta ganin tashe-tashen hankula, inda a cikin kwanaki kasa da bakwai fiye da mutane 60 suka rasa rayukansu.
1181019