Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na kamfanin dilalncin labaran Iba na kasar Iraki cewa, limamin masallacin juma'a na birnin Najaf Sayyid Sadruddini Kubanchi ya bayyana cewa manyan malaman addinin muslunci na birnin Najaf da ke kasar Iraki za su iya bayar da gagaruwar gusnmawa wajen warware rikicin da ake neman a haddasa akasar na banbancin mazhaba ko kabilanci da sauransu da nufin rusa kasar da kuma tsarin da ke tafiya a kansa domin cimam wasu manufofi da wasu kasashen yankin ke son yi dfa hakan.
A bangare guda kuma Fira ministan kasar Iraki Nuri Maliki ya bayyana cewa tun kimanin shekaru biyu da suka gabata a lokacin da aka fara rikicin kasar Syria, shugabna kasar Amurka ya sheda masa cewa shugaba Bashar Assad zai fadi a cikin watanni biyu.
Nuri Maliki ya bayyana hakan ne a zantawarsa da jaridar Sharq Al-ausat ta kasar Masar, inda ya ce a ganawar da ya yi da shugaban kasar Amurka fadar white house shekaru biyu da suka gabata, Barack Obama ya sheda masa cewa a cikin watanni biyu shugaban Syria zai fadi, kamar yadda mataimakin shugaban Amurka Joe Baiden tare da tsohuwar sakataroyar harkokin wajen Amurka Hillary Clinton suka sheda masa hakan, amma Fira ministan na Iraki ya ba su amsa da cewa, shi ya san kasar Syria yadda ya kamata, kuma yan aba Amurka tabbacin cewa Bashar Assad ba zai fadi ko da bayan shekaru biyu ne, balantana watanni biyu.
A bangare guda kuma Nuri Maliki ya soki lamirin gwamntin Turkiya dangane da irin mumunar rawar da take takawa domin rusa kasar Syria, kamar yadda ya ce a halin yanzu kuma tana kokarin ruruta wutar rikici a cikin kasar Iraki saboda wasu dalilai na siyasa, ya ce al’ummar Iraki suna ‘yancin su zabi abin da yake maslaha gare su, Turkiya ba ta hakkin tsoma baki cikin harkokin Iraki na cikin gida da ma sauran kasashen yankin.
1185644