Bangaren kasa da kasa, shugaban kasar Syria Bashar Assad y ace kasarsa ba za ta taba mika kai ga bakaken manufofin Amurka da sauran kasashen yammacin turai kan al’ummar kasar ba domin yin hakan a cewarsa cin amanar al’ummarsa ne kuma za su ci gaba da yin tsayin daka a gaban masu girman kai.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, shugaban kasar Syria Bashar Assad y ace kasarsa ba za ta taba mika kai ga bakaken manufofin Amurka da sauran kasashen yammacin turai kan al’ummar kasar ba domin yin hakan a cewarsa cin amanar al’ummarsa ne kuma za su ci gaba da yin tsayin daka a gaban masu girman kai na duniya baki daya da ‘yan koransu na yankin.
Shuagaba Assad ya bayyana hakan ne a lokacin da yake tarbar wata tawaga daga kasar Jordan da ta kunshi manyna yan siyasa da lauyoyi gami da manema labarai da kuma likitoci da yan jarida, inda ya tarbe sua gidansa da ke birnin Damascus kuma ya basu tabbacin cewa su kwantar da hankalinsu abin da ke faruwa a kasar yan agab da kawo karshe, kamar yadda suma suka nuna cikakken goyon baynasu gare shi kan makircin da yake fuskanta daga Amurka da sauaran kasashen turai da munafukai na yankin.
Bayanin ya ci gaba da cewa shugaban kasar Syria Bashar Assad y ace kasarsa ba za ta taba mika kai ga bakaken manufofin Amurka da sauran kasashen yammacin turai kan al’ummar kasar ba domin yin hakan a cewarsa cin amanar al’ummarsa ne kuma za su ci gaba da yin tsayin daka a gaban masu girman kai irin su Amura da sauransu. 1187151