Bangaren kasa da kasa, an gudanar da tarukan tunawa da ranar demokradiyya a kasar Bahrain wanda manyan bangarorin yan adawa na kasar suka dauki nauyin shiryawa da gudanarwa kamar dai yadda taron ya samu halartar masana daga bangarori na kasar da kuma lauyoyi gami da kungiyoyin kare hakkin bil adama.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar Al-alam cewa, a jiya an gudanar da tarukan tunawa da ranar demokradiyya a kasar Bahrain wanda manyan bangarorin yan adawa na kasar suka dauki nauyin shiryawa da gudanarwa kamar dai yadda taron ya samu halartar masana daga bangarori na kasar da kuma lauyoyi gami da kungiyoyin kare hakkin bil adama na kasar.
A wani labarin kuma shugaban kasar Syria Bashar Assad y ace kasarsa ba za ta taba mika kai ga bakaken manufofin Amurka da sauran kasashen yammacin turai kan al’ummar kasar ba domin yin hakan a cewarsa cin amanar al’ummarsa ne kuma za su ci gaba da yin tsayin daka a gaban masu girman kai na duniya baki daya da ‘yan koransu na yankin.
Shuagaba Assad ya bayyana hakan ne a lokacin da yake tarbar wata tawaga daga kasar Jordan da ta kunshi manyna yan siyasa da lauyoyi gami da manema labarai da kuma likitoci da yan jarida, inda ya tarbe sua gidansa da ke birnin Damascus kuma ya basu tabbacin cewa su kwantar da hankalinsu abin da ke faruwa a kasar yan agab da kawo karshe, kamar yadda suma suka nuna cikakken goyon baynasu gare shi kan makircin da yake fuskanta daga Amurka da sauaran kasashen turai da munafukai na yankin baki daya. 1187149