Kamfanin dilalncin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na tashar Al-alam cewa, kungiyoyin kare hakkin bil adama da wasu bangarori na kasa da kasa suna ci gaba da nuna damuwa dangane da yadda mahukuntan kasar Bahrain suke ci gaba da yin biris da kiran da al'ummar kasar ke yin a neman a yi mulki na adalci kasar maimakon murkushe fararen hula da karfi da masarautar kasar take yi tare da taimakon kasashen yankin.
A nasa bangaren babban magatakardan Majalisar dinkin duniya Ban Ki Moon ya nuna matukar damuwarsa dangane da hukuncin da kotun kolin kasar Bahrain ta tattabar a kan wasu daga cikin 'yan siyasar kasar da kuma masu fafutukar kare hakkin bil adama. Ban Ki Moon ya bayyana cewa abin ban takaici ne yadda mahukuntan Bahrain suka dauki wannan mataki, ya ce ya zama wajibi mahukuntan an Bahrain su cika alkawalin da suka dauka na yin gyara a harkokin shari'a a kasar.
A ranar Litinin da ta gabata ne kotun kolin kasar Bahrain ta tabbatar da wasu hukunce-hukunce da kotun soji ta yanke kan mutane 13, da suka hada da jagororin adawar siyasar kasar, da ma shugabannin kungiyoyin kare hakkin bil adama na kasar da ake tsare da su.
Tun a cikin watan Fabrairun shekara ta 2011 ne al'ummar kasar Bahrain suka fara gudanar da zanga-zangar lumana, inda suke yin kira ga mahukuntan kasar da su gudanar da sauye-sauye na demokradiyya a cikin harkokin siyasa da mulkin kasar, lamarin da mahukuntar kasar suke fuskantarsa da dukaknin karfisu da ma taimakon wasu daga cikin kasashen larabawa, domin murkushe duk wani yunkurin neman sauyi na demokradiyya a kasar.
1187960