IQNA

Al'ummar Kasar Masar Na Ci Gaba Da Nuna Rashin Amincewarsu Da Shugabancin Kasar

12:59 - February 13, 2013
Lambar Labari: 2496041
Bangaren kasa, al'ummar kasar Masar suna ci gaba da nuna rashin goyon bayansu ga morsi,kwana guda bayan kammala taron kungiyar hadin kan kasashen musulmi a kasar Masar, dubun dubatan al'ummar kasar a garuruwa daban-daban sun sake fitowa kan tituna don nuna rashin amincewarsu da gwamnatin shugaban kasar Muhammad Morsi da jam'iyyarsa ta 'yan Ikhwan.

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na jaridar Ahram cewa wasu masu zanga-zangar wadanda suka fito a manyan garuruwan kasar da suka hada da birnin Alkahira, Eskandariya da sauransu, don amsa kiran da 'yan adawar kasar suka yi musu na su fito don nuna rashin amincewarsu da wata fatawar da wani malamin jami'ar Azhar ya fitar da ke kiran da a kashe jagororin 'yan adawa na kasar saboda nuna rashin amincewa da mulkin shugaban Morsin da suke yi lamarin da ya ke ci gaba da fuskantar tofin Allah tsine daga bangarori daban-daban na kasar.
Wasu rahotannin sun ce masu zanga-zangar sun taru a gaban masallacin juma'ar da shugaba Morsi ya yi salla a yau inda suka ta rera taken yin Allah wadai da shi da kuma kokarin kai masa hari a lokacin da ya ke fitowa daga masallacin, lamarin da ya yi sanadiyyar barkewar rikici tsakanin magoya bayansa da masu zanga-zangar, wannan dai shi ne karo na biyu da irin wannan lamari ya faru ga shugaba Morsi a wannan masallacin.
Jam'iyyun hamayya a Masar sun gindaya sharudda uku domin kawo karshen takaddamar siyasar da kasar ke fuskanta. Wata majiyar jam'iyyun siyasar na kasar Masar ta ce; jam'iyyun siyasar sun bijirowa da gwamnatin shugaba Muhammadu Mursi bukatun da idan aka yi aiki da su, za a kawo karshen dambaruwar siyasar da kasar ta ke ciki.

Bukatun sun kunshi yin kwaskwarima akan dokokin aikata laifuka domin su zama masu tsanani akan masu haddasa rikici, da kuma gano masu hannu wajen haddasa rikicin ta hanyar kudade da makamai da kuma gabatar da hotunan rikice-rikicen bayan nan ga babban mai shigar da kara na kasa.

1188000





captcha