Kamfanin dilalncin labaran iqn aya nakalto daga wasu kafofin yad alabarai na kasar Masar cewa, yanzu haka ana gudanar da wani baje koli kan al’adun muslunci a birnin Alkahira na kasar Masar inda ake nuna littafai da wasu daga cikin abubuwan da aka rubuta a cikin addinin muslunci a tarhi gami da suturar musulunci da hakan ya hada nauoin hijabai na mata da dai sauransu.
Majalisar shoora ta kasar Masar zata sake dubawa cikin dokokin gudanar da jerin gwano ta zaman lafiya a kasar a dai dai lokacinda zanga zanga wanda yan adawa suke jagoranta a kasar yake son rikita rayuwa a kasar. A wani bayani wanda kamfanin dillancin labaran AFP na kasar masar ya nakalto daga majalisar a birnin Alkahira, yana cewa a cikin ayoyin dokar jerin gwano dole ne duk wadanda zasu gudanar da jerin gwano su nemi izinin jami’an tsaro kwanaki 5 kafin ranar.
Har’ila yau ya zo a cikin ayoyin dokar cewa yan sanda suka da hakkin hana izinin zanga zanga ga wadanda suka ga zai ruguza harkokin tsaro a kasar. A wani bangare na dokar dai an bawa yansanda damar amfani da hayaki mai sa hawaye ruwan zafi da kuma albarushi don maida zaman lafiya a duk lokacinda ake rikici.
Wasu lauyoyi dai sun yi suka a kan wadan nan dokoki, inda suke cewa kwanaki 5 sun yi yawa ga ma’aikatar cikin gida na ta amincewa wadanda suke bukatar zanga zanga yenta, sun ce yansanda suka bukatar sa’o’I 24 ne kacal na su gudanar da shirye shiryen samar da zaman lafiya a duk wata zanga zanga ta zaman lafiya da za’a gudanar.
1187703