IQNA

Yin Biyayya Ga Umurnin jagora Shi Ne Mabucin Cin Nasara Ga Al'ummar Iran

23:17 - February 17, 2013
Lambar Labari: 2498036
Bangaren kasa da kasa, jagoran mabiya tafarkin Ahlul bait a kasar Farasansa ya bayyana cewa bin umurni da jagora ke bayarwa a cikin dukaknin lamurra shi ne abbabn sirrin nasarar da Iran take samua acikin lamurra duk kuwa da matsin lamabar da take fuskanta a kowane bangare daga kasashen ketare.

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, jagoran mabiya tafarkin Ahlul bait a kasar Farasansa ya bayyana cewa bin umurni da jagora ke bayarwa a cikin dukaknin lamurra shi ne abbabn sirrin nasarar da Iran take samua acikin lamurra duk kuwa da matsin lamabar da take fuskanta a kowane bangare daga kasashen ketare musamman kasashen turai.

Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya yi watsi da tuhumar da ma'abota girman kan duniya suke yi wa Iran na cewa tana shirin kera makaman nukiliya, yana mai cewa Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta yi amanna da wajibcin lalata dukkanin makaman kare dangi da suke duniya.
Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya bayyana hakan ne a lokacin da ya ke ganawa da dubun dubatan mutanen garin Tabriz da ke arewa maso yammacin kasar Iran inda ya ce mu mun yi imani da wajibcin kawo karshen makaman kare dangi a duniya, don haka ne ba ma ma wani kokari wajen kera irin wadannan makamai. Jagoran ya ci gaba da cewa: Idan da a ce muna son kera irin wadannan makaman, to da kuwa Amurka ba ta isa ta hana mu ba.
Ayatullah Khamenei ya kara da cewa: gwamnatin Amurka tana so ne tilasta wa al'ummomin duniya akidunta ne, to amma al'ummar Iran ba za su taba mika kai ga wadannan bakaken manufofi na Amurka ba.
Daga karshe Jagoran ya sake jinjinawa al'ummar Iran saboda gagarumar fitowar da suka yi a lokacin bikin zagayowar shekarar nasarar juyin juya halin Musulunci a kasar inda ya ce irin wannan fitowar yana nuni da riko da koyawar juyin da mutane suke ci gaba da yi ne don kuwa da matsaloli na tattalin arziki da suke fuskanta.
1189778




captcha