IQNA

Wani Malami A Saudiyya Ya yi Kira Da A Daina Cin Zarafin 'Yan shia

23:17 - February 17, 2013
Lambar Labari: 2498037
Bangaren kasa da kasa, wani malamin gwamnatin Saudiyya ya yi kira ga sauran malamai da sauran al'ummar kasar das u daina cin zarafin malaman mabiya tafarkin manzon Allah da iyalan gidansa tsakaka da aka fi sani da shi'a a tsakanin musulmi lamarin day a sanya shi ya fuskanci suka daga malaman wahabiyawa.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, Sheikh hashim Salman wani malamin gwamnatin Saudiyya ya yi kira ga sauran malamai da sauran al'ummar kasar das u daina cin zarafin malaman mabiya tafarkin manzon Allah da iyalan gidansa tsakaka da aka fi sani da shi'a a tsakanin musulmi lamarin day a sanya shi ya fuskanci suka daga malaman wahabiyawa.
Gwamnatin kasar Saudiyya ta yi Allah wadai da harin da jiragen saman yakin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila suka kai kan cibiyar gudanar da binciken sojin kasar Siriya, kafar watsa labaran kasar Saudiyya {SPA} a jiya Litinin ta sanar da cewar Majalisar ministocin kasar Saudiyya ta yi Allah wadai da harin da jiragen saman yakin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila suka kai kan cibiyar gudanar da binciken soji na kasar Siriya tare da bayyana harin a matsayin keta hurumin kasar ta Siriya, kuma wuce gona da iri ne kan daya daga cikin kasashen Larabawa da hakan ya sabawa hadin kan da ke tsakaninsu.
Manazarta na ganin wannan mataki da kasar Saudiyya ta dauka a matsayin nuna fuska biyu a fagen siyasa, a daidai lokacin da take hada kai da manyan kasashen yammacin Turai tare da aikewa da makamai ga 'yan ta'adan kasar Siriya domin ganin bayan gwamnatin Bashar Asad, amma yanzu ta fito tana nuna juyayi kan kasar ta Siriya da haramtacciyar kasar Isra'ila ta kai mata hari bisa cikekken goyon bayan manyan kasashen yammaci musamman Amurka, Faransa da Birtaniya.

1190228





captcha