IQNA

Wasu daga cikin gwamnatocin kasashen turai suna son ganin an warware rikicin Bahrain

23:17 - February 17, 2013
Lambar Labari: 2498038
Bangaren kasa da kasa, wasu daga cikin kasashen yamamcin turai sun nuna bukatar ganin an warware rikicin da ake fama da shia akasar Bahrain ta hanyar tatatunawa tsakanin bangarorin adawa da kuma bangaren gwamnatin kasa da ke iko da dukaknin yankunan kasar.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo, cewa wasu daga cikin kasashen yamamcin turai sun nuna bukatar ganin an warware rikicin da ake fama da shia akasar Bahrain ta hanyar tatatunawa tsakanin bangarorin adawa da kuma bangaren gwamnatin kasa da ke iko da dukaknin yankuna.
A wani labarin kuma mutum guda ya rasa ransa kana wasu da dama sun sami raunuka a kasar Bahrain sakamakon diran mikiyan da jami'an tsaron kasar suka yi wa masu zanga-zangar neman 'yanci a kasar wadanda suka fito kan titunan babban birnin kasar, Manama, don tunawa da shekaru biyu da kaddamar da juyin juya halin neman sauyi a kasar. Rahotannin da suke fitowa daga kasar Bahrain din sun ce sakamakon bude wutan da jami'an tsaron kasar suka yi wa masu zanga-zangar a yau din nan Alhamis hakan ya yi sanadiyyar shahadar wani yaro dan shekaru 16 a duniya mai suna Husain Ali Ahmad Al-Jaziri da kuma raunana wani adadi mai yawa na masu zanga-zangar.

Har ila yau rahotannin sun ce har ya zuwa yanzu ana ci gaba da ba ta kashi tsakanin masu zanga-zangar wadanda suka sha alwashin ci gaba da zama a kan titunan kasar da kuma jami'an tsaron wadanda suke samun goyon bayan sojojin kasar Saudiyya.A ranar 14 ga watan Fabrairun shekara ta 2011 ne dai al'ummar kasar Bahrain din suka kaddamar da juyin juya halinsu na ganin bayan 'ya'yan gidan sarautar Al-Khalifa da suka jima suna zaluntarsu sannan kuma suka ci gaba da wannan yunkuri na su duk kuwa da halin ko in kula da cibiyoyin kasa da kasa suka nuna wa irin zaluncin da ake yi musu.

1189789



captcha