IQNA

Kungiyar kasashen musulmi ta Allawadai da harin da aka kai a garin Quetta na Pakistan

23:26 - February 19, 2013
Lambar Labari: 2499383
Bangaren kasa da kasa, kungiyar kasashen musulmi ta yi Allawadai da ahrin ta'addan cin kasa aka kai kan mabiya tafarkin iyalan gidan manzo a garin Quetta na kasar Pakistan wanda ya yi sanadiyyar yin shadar fararen hula fiye da tamanin a cikin wannan mako.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto aga safin sadarwa na OIC cewa, kungiyar kasashen musulmi ta yi Allawadai da ahrin ta'addan cin kasa aka kai kan mabiya tafarkin iyalan gidan manzo a garin Quetta na kasar Pakistan wanda ya yi sanadiyyar yin shadar fararen hula fiye da tamanin a cikin wannan mako da muke ciki.

Rahotannin da suke fitowa daga kasar Pakistan suna nuni da cewa adadin mutanen da aka tabbatar sun rasa rayukansu a wani harin da aka kai wata kasuwa a birnin Quetta na kasar a jiya Asabar ya karu zuwa mutane 81. yayin da ya ke magana kan hakan kakakin ’yan sandan kasar Pakistan din Fayyal Saumbal ya ce baya ga wadanda suka rasa rayukan na su har ila yau sama da mutane 160 sun sami raunuka. Shi kuma shugaban 'yan sandan lardin Quettan Zubair Mahmud ya shaida wa manema labarai cewa an kai hari ne da wani bomb wanda ya kumshi kimanin ton guda na abubuwa masu fashewa wanda kuma aka boye shi cikin wata tankar ruwa da aka shigo da ita cikin kasuwar da abin ya faru.
A watan Janairun da ya gabata ma dai an kai wani hari makamancin wannan a lardin na Quetta ga jami'an tsaron kasar da kuma wasu mabiya tafarkin Shi'a, inda kimanin mutane 130 suka rasa rayukansu kana wasu da dama kuma suka sami raunuka, lamarin da ya haifar da zanga-zangogi a lardin da kuma wasu larduna na kasar. Wasu rahotannin sun ce kungiyar nan ta 'yan ta'adda ta kasar kasar Pakistan din, Lashkar-e-Jhangvi, ta ce ita ta kai harin.

1191347





captcha