IQNA

An Fallasa Makircin Da Wasu Kasashen Larabawa Suke Kullawa Kasar Syria

20:54 - February 25, 2013
Lambar Labari: 2502380
Bangaren kasa da kasa, gwamnatin kasar Syria ta karyata zargin cewa tana amfani da makamai masu linzami samfurin Skud wajen kai hare-hare kan 'yan bindiga da kasashen yammacin turai ke mara wa baya a cikin kasar.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ministan watsa labarai na kasar Syria Umran Zu'ubi shi ne ya bayyana hakan a jiya a lokacin wata zantawa ta musamman da gidan talabijin din Al-alam, inda ya ce dakarun Syria suna safke nauyin da ya rataya kansu wajen kare kasa da al'ummarta daga 'yan ta'adda da suke samun taimakon kasashen ketare da wasu daga cikin 'yan koransu a kasashen larabawa gami da Turkiya wajen kai hare-hare cikin Syria, amma sojojin na Syria ba su taba yin amfani da manyan makamai kan 'yan wadannan 'yan ta'adda ba, wadanda akasarinsu ba 'yan kasar ta Syria ne ba.

A bangare guda kuma ya karyata jita-jitar da aka kirkiro da ke cewa sojojin Iran da kuma mayakan kungiyar Hizbullah ta Lebanon suna taimakama sojojin Syria wajen murkushe 'yan bindiga a kasar, ya kuma jaddada fatar da gwamnatin kasar take da ita wajen dukkanin bangarorin siyasa na kasar sun koma kan teburin tattaunawa, domin kawo karshen rikicin wanda ya ce dama an shirya shi ne domin rusa kasar kowa ya rasa.
Har ila yau sojojin na Siriya sun yi arangama da wasu ‘yan tawaye masu dauke da makamin a garin Harasta da ke arewa maso gabashin birnin na Damaskus inda bayan nasarar kashe wasu daga cikinsu, har ila yau kuma sun sami nasarar tarwatsa wasu nakiyoyi da bama-bamai da suka dana su a kusa da wata tashar iskar gas na birnin.
A bangare guda kuma a yau ne ake sa ran ministan harkokin wajen kasar Siriyan Walid Mu’allim zai iso nan Tehran don tattaunawa da manyan jami’an kasar ta Iran kan rikicin kasar Siriyan da sauran lamurran da suka shafi yankin nan kafin daga nan kuma zai wuce kasar Rasha don tattaunawa da jami’an kasar kan hanyoyin da za a bi wajen magance rikicin kasar wanda ya shiga shekararsa ta biyu.
1194209








captcha