Bangaren kasa da kasa, kwana guda bayan kama jagoran kungiyar nan ta 'yan ta'adda ta Lashkare Jhanvi da jami'an kasar Pakistan suka yi, 'yan Shi'a na kasar sun bukaci mahukuntan da su gabatar da shi a gaban kotu don yi masa shari'a kan harin ta'addancin da 'yan kungiyarsa suka kai da ya yi sanadiyyar mutuwar sama da mutane 80 a garin Quetta na kasar ta Pakistan.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, yayin da ya ke magana kan hakan, shugaban Jam'iyyar Hazara Democratic Party ta kasar ta Pakistan Abdul Khaliq Hazara ya ce mun jima muna kiran da a kame dukkanin wadanda suke da hannu cikin tada fitinar kabilanci da mazhaba a kasar, ba tare da la'akari da kungiya ko jam'iyyar da suka fito ba. Don haka yace wajibi ne a gurfanar da Malik Ishaq, shugaban kungiyar 'yan ta'addan ta Lashkare Jhanvi a gaban kuliya da kuma yi masa hukumci.
A jiya juma'a ne dai jami'an kasar Pakistan din suka sanar da kame Malik Ishaq din bayan da kungiyar tasa da take da alaka da kungiyar Al-Qa'ida da kuma Taliban ta dauki alhakin kai wasu munanan hare-hare guda biyu kan 'yan Shi'an yankin Quetta cikin 'yan kwanakin da suka gabata da ya yi sanadiyyar mutuwar sama da mutane 180 lamarin da ya janyo rikici da zanga-zanga a duk fadin kasar.
A baya ma dai an taba kama wannan dan ta'addan sai dai kuma an sake shi a matsayin beli duk kuwa da samunsa da hannu dumu-dumu cikin kisan gillan da aka yi wa wani adadi mai yawa na mutanen kasar.
1194047