Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, nNabil Qawuq ya ci gaba da cewa Isra'ila da masu kare ta a duniya sun zage damtse domin fitar da kasar Syria daga kan layin gwagwarmaya, sai dai har yanzu ba su sami nasara ba." Har ila yau, mataimakin shugaban majalisar zartarwar na Hizbullah ya ce; shekaru talatin kenan da H.K. Isra'ila ta ke mafarkin kawo karshen kungiyar HIzbullah, sai dai a kowace rana ta Allah gwagwarmayar tana kara karfi. Nabil Qawuk ya ci gaba da cewa; Tare da cewa H.k. isra'ila ce ta ke bai wa 'yan ta'addar kasar Syria makamai da kudade, amma duk da haka har yanzu Syrian kasa ce ta gwagwarmaya.
Babban magatakardar Kungiyar HIzbullah ta Lebanon Sayyid Hasan Nasarallah, ya jaddada cewa; Gwagwarmaya ba za ta yi shiru akan duk wani hari da za a kawo ma ta ba. A dazu da ya ke gabatar da jawabi na shekara-shekara domin tunawa da jagororin kungiyar da su ka yi shahada, Sayyid Hasan Nasarallah ya gargadi Isra'ila da kuma masu daure mata gindi akan cewa; idan har su ka kai wa Lebanon hari, to gwagwarmaya ba za ta yi shiru ba." Babban magatakardar kungiyar ta Hzibullah ya ci gaba da cewa; Kungiyar gwagwarmaya tana cikin shiri, kuma dukkanin abubuwan da ta ke bukatuwa da su suna cikin Lebanon.
Sayydi Hasan Nasarallah ya ce; Haramtacciyar Kasar Isra'ila tana sane da cewa abinda mu ke fada gaskiya ne, shi ya sa ta ke kokarin yin kutse da 'yan leken asirinta da kuma aikewa da jragen leken asiri da na yaki. Babban magatakardar kungiyar ta Hizbullah ya kuma jaddada nasarorin da gwagwarmaya ta samu a cikin shekaru talatin da su ka gabata, abinda ya maida ita mai tsayuwa da kafafunta ba mai mafarkin tsaye ba.
1198009