Bangaren kasa da kasa, batun matasalar da palastinawa suke ciki na fuskantar zaluncin haramtacciyar kasar Isra’ila shi ne babban abin da ya hada dukaknin muslmi da mahangarsu a duniya duk kuwa da banbanci a wasu bangarorin.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga bangaren yada lbaransa aTehran cewa, shugaban majalisar koli ta tsaron kasar Iran Dr Saeed Jalili ya bayyana matsalar kasar Palasdinu a matsayin matsala wacce take hada kan musulmi a duk fadin duniya.
Jalili ya bayyana haka ne a jiya a lokacinda yake ganawa da shugaban ofishin kungiyar gwagwarmaya ta Hanas a nan Tehran Musa Mohammad Abu Marzook. Gwagwarmayan da Palasdinawa suke jagoranta wajen fada da mamamayar da yahudawan Sahyoniyya sukewa kasar Palasdinu zai zaba sanadiyyar hadin kan musulmi kuma zai hana barkewan rigingimu a tsakaninsu. Sa’aedd Jalili ya kara jadda cewa gwamnatin JMI zata ci gaba da goyon bayan kungiyoyi masu gwagwarmaya da mamayar HKI. A nashi bangaren Musa Mohammad Abu Marzook ya yaba da irin taimakon da kungiyarsa ta HAMS take zamu daga bangaren JMI, sannan yay i fatan za’a warware rikicin da ke faruwa a kasar Syria tare da kokakrin da manyan manyan kasashen yankin suke yi don kawo karshen rikicin.
Y ace al-ummar Palasdinu sun cutu kwarai da rikicin da ke faruwa a kasar Syria sannan suna fatan za’a a gabayansa nan ba da daewa ba.
1198841